Connect with us

Labarai

Covid-19: Yadda gwajin Corona ke tafiya a Kano

Published

on

Tun bayan bullar cutar Covid-19 a Kano a kan samu wasu ranaku da ba a samu karin wadanda a ka gano su na dauke da cutar ba.

Ko a ranar Asabar 16 ga watan Mayun da mu ke ciki, ba a samu ko mutum guda dake dauke da cutar ba a Kano, haka abun yake a ranar Talata 19 ga watan Mayun.

Farfesa Isah Sadiq Abubakar shi ne shugaban sashen gwaje-gwajen cututtuka masu yaduwa na jami’ar Bayero dake jihar Kano, domin jin shin ko hakan ya na nufin an tasamma kassara cutar a Kano?

Ya ce “A’a ba za mu yi saurin daukar hakan ba, domin yin hakan zai zama wani ganganci, domin idan a ka dauka anyi nasarar dakile wannan cuta tun yanzu to kaga mutane za a yi sake, daga mu masu yakar abun zuwa mutanen gari. Ganin cewa ba a samu case ba na kwana daya abu ne da zai faranta mana rai, amma kuma kwana daya ba komai bane a wannan yaki, har sai in an samu hakan ya dore zuwa wani lokaci, mun ga cewa abun ba a samun bullar cutar shi ne  za mu yi wannan murna cewa an fara samun nasara”.

Ko a kwai mutanen da ku ka yi wa gwaji a ranar Asabar din kuma a ka samu basa dauke da cutar, domin haka ya zama “0 Case” ko yaya?

“To akwai dakunan gwaji guda 3 a Kano, amma na san a dakin da nake shugabanci na jami’ar Bayero ba muyi gwajin Kano ko guda daya ba a wannan rana, ban san sauran dakunan gwajin ba. Mu a wurin mu ranar mun yi aikin da a ka aiko mana daga jihohin Katsina da Jigawa, amma Jigawa sun aiko guda 600, Katsina kuma sun aiko da guda 200 to sai ranar Lahadi mu ka yi aikin na Kano”.

A kididdigar da ku ke fitarwa ta adadin wadanda su ka kamu ko su ka warke a kullum, ko akwai yi wuwar ku rika fitarwa dauke da adadin wadanda ku ka yi wa gwaji a kullum, a cikin su ga wadanda su ka kamu domin jama’a su rinka rarrabewa?

 

“Eh, ya kamata dai kam, wannan tsari ne me kyau kuma kwamiti na jiha zai yi hakan nan bada jimawa ba. Inji Farfesa Isah.

Tattaunawar mu da Farfesa Isah Sadiq Abubakar shugaban sashen gwaje-gwajen cututtuka masu yaduwa na jami’ar Bayero dake jihar Kano.

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Labarai

Dilolin Wiwi sun yanki mai unguwa da Wuƙa, tare da cizon shi a hannu, kan ya shana su sha da siyar da wiwi a Kano

Published

on

Wasu matasa da ake zargin ƴan Daba ne, kuma dilolin Wiwi, sun kai wa mai unguwar yankin Bachirawar Tukwane ƙarshen kwalta hari da muggan makamai.

Tun farko dai mai unguwar yankin Malam Mustapha ya shawarci matasan ne, da su dai na ɗaurin tabar Wiwi, da siyar wa a kofar gidajen mutane lamarin da ya tunzura matasan.

Matasan dai sun rutsa mai unguwar Bachirawar ne inda suka yi yunƙurin hallaka shi, bayan da suka yanke shi da Wuƙa, tare da cizon sa a Hannu, sai dai ‘yan ƙungiyar bijilante na yankin sun kawo masa ɗauki inda suka kama wani matashi mai laƙabin Kokuwa.

A lokacin ne kuma mutanen yankin suka yi yunƙurin ɗaukar doka a hannu, sai dai mai unguwar Bachirawa Malam Mustapha dan Bachirawa Gabas Malam Abdulkadir Dandiyo, sun kuɓutar da matashin inda aka mika shi ofishin ƴan sanda, ragowar matasan suka tsere.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin Dakta Jibrin Sagir, ya ce a shirye suke su tinkari duk wani ɓata gari a yankin da yake addabar su.

Continue Reading

Trending