Connect with us

Labarai

Marayu da gajiyayyu sun samu tallafin Ramadan -Kayarima

Published

on

Kungiyar hada zumunci me rajin tallafawa marayu da gajiyayyu, ta ce dole ne al’umma masu karfi dake makwabtaka da marayu sai sun kyautatawa marayun da kuma marasa karfi a cikin yankunan su domin rage masu radadin halin da su ke ciki a wannan lokaci na kullen lockdown.

Shugaban kungiyar, Muhammad Abdulsalam Kayarima ne ya bayyana hakan a lokacin da kungiyar ke rabon tallafin kayan abinci ga marayu da kuma marasa karfi a yankin karamar hukumar Kumbotso da Tarauni a yau Laraba.

Kungiyar ta je gidan marayu masu aikin wankau a Kano

Muhammad Abdulsalam Kayarima, ya ce” Makasudin wannan tallafin shi ne mu tallafawa mabukata tare da marayu dake fadin jihar Kano. Domin akwai marayu wadanda su ke cikin wani hali a wannan lokacin, dole sai al’umma sun fito domin tallafawa marayun dake kusa da su domin rage masu radadi tare da jawo su a jiki”. Kayarima.

Kayan abinci shinkafa da taliya da kuma man girki.

Wannan shi ne karo na biyu da kungiyar ta yi rabon tallafin a cikin watan Azumin Ramadan, sai dai a wannan karin kungiyar ta raba kayayyakin abinci na mabukata 70 ciki harda Atamfofi da kuma dinkakkun kayan sawa na mutum biyar maza. Haka zalika kungiyar ta kuma baiwa marayun nan wanda su ke aikin wankau tallafi domin rage masu radadin tallauci da su ke fama.

Wata mata da ta samu tallafin a Kano.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

An kama wani matashi da zargin sacewa almajirai kayan sawa

Published

on

Shugaban kungiyar Bijilante na yankin unguwar Hausawa dake karamar hukumar Tarauni a Kano, Usaini Haruna Kailo, ya shawarci iyaye da su kara kulawa da tarbiyyar ya’yan su domin rayuwar su ta zama abar koyi a nan duniya dama ranar gobe kiyama.

Usaini Kailo ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u, bayan kama wani matashi da su ka yi, da zargin diban kayayyakin sawa na almajirai cikin wata makarantar tsangaya a unguwar Hausawa ‘yan babura.

Ya ce” Matukar iyaye za su kara kulawa da tarbiyar ya’yan su babu shakka za a rage yawaitar samun lalacewar su”.

Da yake nasa jawabin matashin da a ka kama ya ce” Wannan shi ne na farko kuma shi ne na karshe ba zan kara satar kayayyakin mutane ba”.

Wakilin na mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito mana cewa, Kwamandan Bijilanten Usaini Haruna Kailo ya ce, za su mika matashin da su ka kama wajen jami’an tsaro domin matakin da ya dace a kan sa domin hakan ya zama izina ga sauran matasa.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Gwamnatin Kogi ta karyata hukumar NCDC

Published

on

Gwamnatin Jihar Kogi ta musanta rahoton hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC cewa mutum biyu sun kamu da cutar Coronavirus a jihar.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai hukumar ta NCDC ta sanar a shafinta na Twitter cewa an samu bullar cutar Covid-19 a jihar ta Kogi inda tace mutane 2 ne ta tabbatar sun kamu da cutar a jihar.

Sai dai a cikin wata sanarwa da kwamishinan lafiya na jihar ta Kogi, Dakta Saka Haruna Audu ya musanta rahoton, inda sanarwar ta bayyana rahoton na NCDC a matsayin labarin kanzon kurege ne da bashi da tushe balantana makama.

Ya ce” A shirye gwamnatin Kogi ta ke wajen kare rayukan al’ummar ta, kuma ba za ta sanya siyasa a cikin sha’anin kiwon lafiya a jihar ba”.

Sai dai hukumar NCDC ba ta ce komai ba dangane da ikrarin na gwamnatin jihar Kogi.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Buhari ya nemi sake ciyo bashi

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake aikewa da wata wasika ga majalisar wakilai domin sahale masa ya ciyo bashin dala Biliyan 5.

Wasikar da shugaban majalisar wakilan Femi Gbajabiamila ya karanta a gaban majalisar a yau alhamis, ta bayyana cewa, za a yi amfani da bashin ne domin cike gurbin kasafin kudin bana, na manyan ayyuka.

Kazalika ta cikin wasikar shugaban ya kuma ce za a yi amfani da bashin wajen kara tallafawa jihohi domin yaki da cutar corona.

A kwanakin bayane dai majalisa ta sahalewa shugaban kan ciyo wasu bashi na biliyan 22.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish