Connect with us

Labarai

Wasu da a ke zargi da satar Tumakai sun shiga hannu a Kano

Published

on

Kotun Majistret mai lamba 72 karkashin mai shari’a, Aminu Gabari ta aike da wasu mutane 3 zuwa caji ofis domin a garkame su.

Tun da farko dai a na zargin wani jami’in Co-operate Security mai suna Sahabi Nafi’u da laifin sojan gona da hada baki domin aikata laifi da kuma laifin hallattawa kansa kayan sata.

Kunshin tuhumar ya bayyana cewar Sahabin ya yi sojan gona ya bayyana kansa a matsayin dansanda ya kuma kwace wasu tumaki 9 wadanda a ke zargin wasu Fulani sun sato ya kaiwa abokin sa ajiyar su.

A yayin da a ka gabatar da su a gaban kotun mai, shari’a Aminu Gabari ya yi umarnin ‘yan sanda su tsare su, kuma a gobe ne za a karanta mu su kunshin zargin da a ke yi mu su.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya zanta da su harma daya daga cikin su ya bayyana cewar shi ne ma ya tseguntawa jami’an security cewar ga barayin tumaki, amma daga karshe sai ya ga an alkinta su.

Labarai

Masu koyarwa a aji su ci gaba da zama a gida – KSSSMB

Published

on

(more…)

Continue Reading

Labarai

Mu godewa Allah a kan jarabawar da ya dora mana – Limamin Madina

Published

on

Limamin masallacin Madina Sheikh Aliyu Abdul Rahman Al Hudaifyi ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su rungumi dabi’ar yin hakuri duba da yadda Allah ke jarrabar su da ibtila’i daban-daban.

Sheikh Hudaifyi ya bayyana hakan ne ta cikin hudubar juma’a dake zuwa kai tsaye a tashar Dala wanda Malama Maryam Abubakar take fassara wa.

Ya ce” Kamata al’ummar musulmi su rinka yin godiya ga Ubangiji a dukkanin jarrabawar da Allah ya jarrabe su da ita, duk mutumin da yake hakuri to Allah zai ba shi lada mai yawa”.

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewa Sheikh Aliyu na cewa ya kamata mutane su dage da addu’o’in samun sauki a dukkannin al’amuran rayuwa.

Continue Reading

Labarai

Tun da ba zuwa aikin Hajji ku taimakawa masu da’awa – Liman

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Ihya’us Sunnah da ke kofar Nasarawa, Malam Anas Abbas Ibrahim ya ce, Tun da a bana ba a samu damar zuwa aikin Hajji da Umara ba, kamata ya yi masu hali su tallafawa kungioyi da kuma al’ummar da su ke fita wa’azi na musuluntar da wadanda su ke ba musulmai ba.

Malam Anas Abbas Ibrahim ya bayyana hakan ne a hudubar da ya gudanar a Juma’ar nan.

Ya ce, “Manzon Allah (S.W.A) an taba hana shi ya yi aikin Umara, wanda hakan ya jawo a ka yi sulhu  a Hudaibiya, bayan anyi sulhun ya hakura, daga nan shi da Sahabban sa su ka himmatu domin jawo mutane su shigo musulunci, manzon Allah (S.W.A) da kan sa ya rubuta wasiku ya aikawa sarakunan duniya, kamar sarkin Farisa da kuma sarkin Rum”.

Malam Anas ya kara da cewa, “A shekarar da a ka yi sulhun ne kuma wadanda su ka shiga musuluncin sun ninka wadanda su ka shiga gabanin haka”. A cewar Malam Anas Abbas

Wakilin mu Tijjani Adamu ya rawaito cewa, Malam Anas ya kuma ja hankalin samarin da su ke hawa dandalin sada zumunta, su yi kokarin yada abubuwa kyayawa na musulunci tare da kiran mutane zuwa musulunci.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish