Connect with us

Labarai

Covid: An fara sakin mutanen da ake zargi da aikata manyan laifuka a Kano

Published

on

A yunkurin ta na dakile yaduwar cutar Coronavirus gwamnatin jihar Kano ta fara sakin mutanen da a ke zargin sun aikata manyan laifuka domin rage cinkoso a gidajen gyaran hali.

Lauyoyin gwamnati, Zahraddin Kofar Mmata da Maryam Muhammad Jibrin su ne su ka bayyana rokon a saki mutanen a gaban mai Shari’a Haulat Magaji Kankarofi ta kotun Majistret mai lamba 57 kuma nan take kotun ta karbi rokon lauyoyin.

Da take kwarya-kwaryar hukunci mai Sharia Haulat ta bayyana cewar ta amince da rokon lauyoyin gwamnatin tun da dama su ne su ka shigar da karar.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Ismail ya zanta da wani matashi mai suna Auwalu Isah wanda ya ce” Ni a na zargi na da laifin kisan kai yau shekaru 5 kenan ga shi yanzu an sallame ni”.

Shi kuwa Dan Bello Sule Makoda cewa ya yi” Ana zargina da laifin kisan kai sai gas hi yanzu an sake ni bisa taimakon gwamnati na yi shekaru hudu a gidan Yari hudu kuma gidan iyaye na”.

Wani lauya mai zaman kansa, Barrister Mu’aruf Yakasai ya bayyana cewar” Matakin da gwamnatin ta dauka ya dace, domin an kai wasu da a ke zargi gidan yari ba tare da an yanke masu hukunci ba, irin wadannan shari’ar a ka tace an saka su a hannun belli, amma idan za a ci gaba da shari’ar za su dawo ba wai a na nufin shari’ar ta kare ba kasha 90 wadanda ke gidan ajiya da gyaran hali irin su ne a ciki”

Wakilin mu Yusuf Nadabo ya bayyana cewar cikin mutanen da a ka saki sun hadar da Nasiru Salisu da Baffa Muhammad, da Auwal Isah da Abdullahi sule sai kuma Laurence Abilah.

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Labarai

Dilolin Wiwi sun yanki mai unguwa da Wuƙa, tare da cizon shi a hannu, kan ya shana su sha da siyar da wiwi a Kano

Published

on

Wasu matasa da ake zargin ƴan Daba ne, kuma dilolin Wiwi, sun kai wa mai unguwar yankin Bachirawar Tukwane ƙarshen kwalta hari da muggan makamai.

Tun farko dai mai unguwar yankin Malam Mustapha ya shawarci matasan ne, da su dai na ɗaurin tabar Wiwi, da siyar wa a kofar gidajen mutane lamarin da ya tunzura matasan.

Matasan dai sun rutsa mai unguwar Bachirawar ne inda suka yi yunƙurin hallaka shi, bayan da suka yanke shi da Wuƙa, tare da cizon sa a Hannu, sai dai ‘yan ƙungiyar bijilante na yankin sun kawo masa ɗauki inda suka kama wani matashi mai laƙabin Kokuwa.

A lokacin ne kuma mutanen yankin suka yi yunƙurin ɗaukar doka a hannu, sai dai mai unguwar Bachirawa Malam Mustapha dan Bachirawa Gabas Malam Abdulkadir Dandiyo, sun kuɓutar da matashin inda aka mika shi ofishin ƴan sanda, ragowar matasan suka tsere.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin Dakta Jibrin Sagir, ya ce a shirye suke su tinkari duk wani ɓata gari a yankin da yake addabar su.

Continue Reading

Trending