Connect with us

Labarai

Covid-19: An janye karbar haraji har tsawon watanni biyu saboda Corona

Published

on

Karamar hukumar Doguwa ta janye karbar haraji ga ‘yan asalin karamar hukumar tsawon watanni biyu domin su farfado daga kangin da korona ta jefa su.

Shugaban karamar hukumar Doguwa, Ali Abdul Ali, ya bayyana hakan lokacin kaddamar da tallafin kayan abinci karo na biyu da gwamnati ta gabatar domin ragewa masu karamin karfi radadin zaman gida.

Shugaban karamar hukumar wanda mataimakin sa, Dauda Hamisu Falgore, ya ce” Mun yi la’akari ne da kasancewar mazauna karamar hukumar manoma ne da ‘yan kasuwa”.

A nasa jawabin gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar bada agajin gaggawa da tsugunar da gajjiyayyu ta Jihar Kano, Sale Aliyu Jili, ya ce” Za a ci gaba da rabon tallafin karo na Uku ga masu bukatar da su ka cancan ta”.

Da Ya ke nasa jawabin Hakimin karamar hukumar Doguwa, Alhaji Abdullahi Iliyasu, ya yabawa ‘yan kwamitin tare da hakurkurtar da wanda ba su samu ba.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewa ‘yan kasuwa da wadan da su ka amfana da tallafin sun bayyana godiyar su.

Labarai

Rahoto: Annabi (S.A.W) zababbe ne a cikin halittu – Limamin Gwazaye

Published

on

Limamin masallacin Ammar Bin Yasir dake unguwar Gwazaye Gangar Ruwa, Malam Zubairu Almuhammady, ya ce Annabi (S.A.W) zababbe ne a cikin halittu, domin ya na daga fifikon sa, ya na gani ta bayan sa kamar yadda ya ke gani ta gaban sa.

Malam Zubairu ya bayyana hakan ne a hudubar Juma’a da ya gabatar ya na mai cewa, Dukkanin halittun duniya su na bayan manzon Allah (S.A.W), saboda haka al’umma mu yi koyi da shi, domin haduwa da Allah lafiya.

Domin jin cikakken bayanin hudubar saurari wannan.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Ubangiji ya yi wa Annabi darajar da babu wanda ya ke da ita – Limamin Maidile

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Jami’u, Sheikh Aliyul Qawwas dake unguwar Maidile a karamar hukumar Kumbotso, Malam Muhammad Kamaludden Abdullahi Maibitil, ya ce manzon Allah (S.A.W) shi ne shugabannin dukkanin Annabwa, kuma ubangiji ya girmama shi da girman da ya kadaita shi a kan Annabin kadai.

Muhammad Kamaludden, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa gidan rediyon Dala FM, karin bayani kan abin da hudubarsa ta kunsa.

Domin cikakken bayanin hudubar saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mai hakuri zai rabauta da rahamar Ubangiji – Limamin Bachirawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Malam Adamu Babarbare dake unguwar Bachirawa, Malam Muhammad Yakubu Madabo, ya yi kira ga al’ummar musulmi da su kasance masu hakuri da juriya a cikin rayuwar su, domin rabauta da falalar ladan masu hakuri.

Malam Muhammad, ya bayyana hakan ne ta cikin hudubar juma’a da ya gabatar ya na mai cewa, masu hakuri za su rabauta a duniya da lahira, domin Allah ya tabbatar da zai jarrabi bayin sa, amma idan su ka yi hakuri za su dace da rahamar sa.

Mu na da cikakken bayanin hudubar ta cikin wannan murya dake kasa.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!