Connect with us

Labarai

Covid-19: Kungiyar lauyoyi ta koka dangane da cinkoson SARS

Published

on

Kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Kano (NBA) ta koka bisa yadda su ka ga cinkoson mutane a sashin bincike na ‘yan sandan SARS Kano.

Sakataren kungiyar, Barrister Mujitaba Adamu Ameen wanda ya ja tawagar lauyoyin zuwa shelkwatar hukumar gyaran hali domin su mika wannan kuka tun da dai ‘yansandan sun ce gidajen yari duk a kulle su ke.

Barrister mujitaba ya bayyana cewar “Yan sanda ba su da hurumin rike mutum har ya yi kwanaki a hannun su, domin abun tausayin ya isa al’umma ne jibge a ciki wadanda a ke zargi da laifin kisa da aikiata fashi da makami, duk da wannan lalurar ta Covid-19, kuma mutanen ba zai yu a sake su ba, sai dai mun nemi hukumar shari’a ta jihar Kano domin ba mu goyon bayan an rage cinkoso. Sai dai shugaban hukumar gidan ajiya da gyaran hali ya yi na’am damu, tun da a ciki za a samar wajen killace mutum gudun kada ya shafawa na ciki cutar”.

Ya yin da yake martani shugaban hukumar gidajen gyaran hali na Kano, Alhaji Ahmad Magaji ya bayyana cewar” Mun kulle gidajen ne domin tsoron kada korona biros ta barke a cikin gidan, amma a na gab da budewa da zarar an gina cibiyar killace mutane a gidan yarin”.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito cewar tuni kotunan Majistret da hadin gwiwar ma’aikatar shari’a su ka fara sakin wadanda a ke zargi da manyan laifuka domin rage cinkoso.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending