Labarai
Magidanci ya yi wa matar sa dukan kawo wuka a kan sallah

Wani magidanci mai suna Muhammad Rabi’u dake unguwar Bachirawa a yankin Darerawa, karamar hukumar Fagge, ana zarginsa da yiwa matarsa Maryam dukan kawo wuka a cikin dare saboda ta yi masa nasiha akan ya rinka yin sallah.
Wakilin mu Abubakar Sabo ya zanta da wani makwabcin magidancin, wanda suka kubutar da matar ya ce, “Muna kofar gida sai naga mace ta fito kusan babu kaya a jikinta, sai naje muka shiga cikin gida aka bata kaya ta saka”. A cewar Makwabcin Magidancin.
Itama wata makwabciyar ma’auratan, ta bayyana yadda al’amarin ya faru, “Mu dai muna cikin gida muka rinka jin ihu, sai muka ce ko wata ce ta tayar da aljanu, muna fitowa sai muka ga mace daga ita sai siket, ta na cewa, mjinta ne yake ikirarin sai ya kashe ta, saboda ta ce yayi sallah, sai mu ka ce ta shigo aka bata kaya ta saka”. Inji Makwabciyarsu.
Kazalika, Aminiyar matar, ta bayyanawa wakilin namu irin zaman da matar take yi da mijin nata, “Dama batun yau ba ta na gaya min abubuwan da yake mata, kodaysushe in ta fada min na kan ce tayi hakuri. Ta tura aka kira ni nazo naga mijin nata yayi mata rauni, to gaskiya ya kamata ace hukuma ta shiga ciki, abi mata hakkinta. A cewar Aminiyar Maryam.
Maryam matar magidancin Muhammad Rabi’u, ta bayyana mana yadda al’amarin ya faru da cewa, “Bayan Magriba ya shigo, na ce ba za ka yi sallah ba ne? Nayi magana ka yi Azahar baka yi ba, ka ce za ka yi, La’asar ba ka yi ba, shi ne ya ce, zan koya masa sallah ne? ya dauke ni da mari ya ce, zan nuna masa musulunci ne? Ya buga min tabarya, na ce zai kashe ni ne? Ya ce, in bashi dukiyar aurensa, ya ce, zai kashe ni yaga mai tsaya min”.
Ko yana shaye-shaye?
“Ya na shaye-shaye, ya na shan wiwi, har ma naga kwaya al’ajihunsa, har ma zai shigo ya fadi, kuma ya na min kashi a wando, nayi masa nasiha, baya salla baya azumi, ya ce zai gyara, ashe bai gyara din ba”.
Dama kin san ya na haka kika aure shi?
Maryam ta kara da cewa, “A’a ban sani ba. ya daki kaina ya hada da gini, ina ihu ya toshe bakina, na samu na kufce ya bini soro ya kama ni ya na jana, shi ne na dauki buta na ce zan je ban daki, na samu na zo soro na yarda butar daga ni sai siket, na fito wajen mutane na ce su taimaka min. Inji Maryam.
Maryam ta ce, ta hakura da auren, ta kuma nemi mahukunta da su taimaka su raba auren nasu, ta kuma yi wa sauran mata nasiha da su rinka gudanar da bincke kafin su yi aure.

Labarai
Kisan gillar Edo: A gaggauta nemawa mutanen da aka kashe haƙƙin su, ko mu ɗauki Mataki bisa doka – Human Rights

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network, ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta Kano da kuma ta jihar Edo, da gaggauta neman haƙƙin Mafarautan nan ƴan asalin jihar Kano waɗanda aka yi wa kisan gilla a garin Uromi na jihar Edo.
Daraktan ƙungiyar na ƙasa Kwamared Gambo Madaki shi ne ya bayyana wa tashar Dala FM Kano, hakan a ranar Litinin, lokacin da yake tsokaci kan kisan sama da Mafarauta 16 a jihar Edo, waɗanda suka taho daga jihar Ribas za su dawo gida Kano.
Ya ce baya ga ɗaukar matakin lalubo waɗanda suka aikata rashin imanin, akwai buƙatar a ɗauki mummunan mataki akan su don daƙile afkuwar irin hakan a gaba.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ɓatabgari ne su ka damke wadanda abin ya shafa a Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas ta Jihar Edo, inda su ka ga bindigogin farauta, sai kawai su ka yanke cewa ai masu garkuwa da mutane ne, inda suka kona su da ransu a ranar Alhamis.
Lamarin dai ya jawo cece-ku-ce, inda ‘yan Najeriya da dama ke zargin gwamnati da gazawa wajen dakile irin wannan ɗaukar doka a hannu.
A cewar Gambo Madaki, baya ga batun kafa kwamiti da gwamnatin Kano ta yi akan wannan batun, ya kamata gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙara bibiyar lamarin da kan sa, don ganin an ɗauki matakin da ya dace akan kisan gillar ko kuma su ɗauki mataki bisa doka.

Labarai
Mun baza jami’an mu lungu da saƙo don samar da tsaro yayin bikin Sallah a Kano – Anty Snaching Phone

Rundunar tsaron nan da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Waya da kuma dakile Shaye-shayen kayan maye, ta Anty Snaching Phone, ta ce ta baza jami’an ta kusan dubu ɗaya da za su shiga lungu da saƙo na jihar nan, domin samar da tsaro a yayin bukukuwan ƙaramar Sallah.
Kwamandan rundunar a nan Kano Inuwa Salisu Sharaɗa ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Freedom Radio, ya kuma ce jami’an su za su yi duk mai yiyuwa wajen daƙile ayyukan ɓata garin da ke shirin tayar da hankalin al’umma yayin bikin sallar.
“Daga cikin jami’an mu da za su samar da tsaron akwai na cikin kayan mu da kuma na farin kaya, kuma sun fara bazama guraren da mu ka tura su tun cikin kin daren Asabar ɗin nan kuma za su yi aiki cikin ƙwarewa kamar yadda suka samu horo, “in ji Inuwa”.
Sharaɗa, ya kuma ce hakan na cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano ƙarkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa kulawar shugaban kwamitin karta-kwana da ke yaƙi da miyagun ɗabi’u da gwamnan ya kafa ƙarkashin Dakta Yusuf Ƙofar Mata.
Wannan dai na zuwa ne yayin da za’a gudanar da sallar Idi, ta ƙaramar Sallah a ranar Lahadin nan a Najeriya, da Jamhuriyyar Nijar da ƙasar Saudiyya, da ma wasu ƙasashen Duniya.

Labarai
Za a cika Azumin Ramadan na shekarar 1446 guda 30 – Masani

Wani masanin ilmin Taurari da ke jihar Kano a arewacin Najeriya, Mallam Nasir Falaki Al-Kanawi, ya ce za a cika Azumin Ramadan na shekarar 1446 guda 30 saboda watan Shawwal ba zai ganu ba a ranar Asabar, don da ƙarfe 11:58 na safe za a haifi jinjirin watan kuma zai faɗi 06:48 na Yamma.
Mallam Nasiru Alfaki Al-Kanawi ya bayyana hakan ne a wani taƙaitaccen jawabi da ya yi wa gidan rediyon Dala FM Kano a ranar Juma’a 28 ga watan Maris ɗin shekarar 2025.
Alfalaki ya kuma ce watan zai faɗi ne da ƙarfe 6:48 na yamma mintuna kasa da 10 kenan bayan faduwar Rana, kasancewar ranar ƙarfe 6:37 na yamma za ta fadi.
Ya ci gaba da cewa to wannan dalilin ne zai sa watan ba zai ganu ba, ko da kuwa da Na’ura ne kasancewar bai samu wadataccen hasken da zai ɗosana daga ranar ba, wanda aƙalla yana buƙatar awanni 13 zuwa 16 daga haifeshi kafin ace an iya ganinsa, Allah shi ne mafi sani Mai iko akan komai.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su