Connect with us

Manyan Labarai

Premier League: Za a yi wasan hamayya a filin wasa na Goodison Park

Published

on

Hukumar shirya gasar Firimiya ta kasar Ingila ta tabbatar da cewa za a yi wasan hamayya tsakanin Everton da Liverpool a filin wasa na Goodison Park.

Wasan dai na daya daga cikin wasannin Liverpool me jan hankali dazarar an dawo gasar Premier.

Haka zalika Liverpool an bata damar yin wasannin ta a cikin filin ta na Anfield.

A ranar 21 ga watan nan ne za a dawo gasar yayin da Liverpool keg aba a kan teburi da maki 25.

Wannan dai shi ne damar ta ta farko da za ta daga gasar a karon farko tun cikin shekara 30.

Manyan Labarai

Wasu ma’aurata sun rasa ransu a wata gobara da ta kama a Kano.

Published

on

Hukumar kashe Gobara ta jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wasu ma’aurata bayan da wuta ta ƙonesu a lokacin da Gobara ta kama a ɗakuna biyu da ke gidan su, a garin Rangaza da ke ƙaramar hukumar Ungogo a jihar Kano.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikowa Dala FM, a yau Juma’a 13 ga watan Disamban 2024.

Ya ce gobarar ta kama ne a gidan cikin daren jiya Alhamis, inda suka samu kiran gaggawa daga wani jami’in su mai suna FS Ahmad Abubakar da misalin ƙarfe 01:45 na dare, lamarin da jami’an nasu suka kai agajin gaggawa.

“Ana sanar da mu lamarin ne jami’an mu na Bompai suka garzaya gidan da lamarin ya shafa inda suka ƙarasa da ƙarfe 01:51, tare da kashe wutar ba tare da ta tsallaka maƙota ba, “in ji Saminu”.

Kakakin hukumar ya kuma ce baya da jami’an nasu suka kai miji da matar Asibiti ne likitoci suka tabbatar da rasuwar su, bayan da wutar ta ƙone su.

“Ma’auratan sun haɗar da Muhammad Uba mai shekaru 67, da kuma matar sa mai suna Fatima Muhammad, mai shekaru 52, “a cewar Saminu”.

Ya ƙara da cewar tuni jami’an nasu suka miƙa mamatan ga mai unguwar yankin Muhammad Auwalu Rayyanu, domin zuwa ayi musu sutura, yana mai cewa suna ci gaba da bincike domin gano musabbabin tashin gobarar.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha sun jingine yajin aiki a Kano

Published

on

Ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano, sun jingine yajin aiki da suka shiga daga ranar Talata, sakamakon zargin da suka yi na gaza fara basu sabon tsarin mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 71,000, da kuma wasu zarge-zarge da suka yi.

Sakataren ƙungiyar ma’aikatan hukumar samar da ruwan a jihar nan Muntari Ado Tattarawa ne ya bayyana wa Dala FM hakan, ya ce sun janye yajin aikin ne yau Alhamis, sakamakon zaman da suka yi ranar Laraba, da babban sakataren ma’aikatar ruwa, da shugaban ma’aikatan jihar Kano, da kuma shugabancin ƙungiyar ƙwadago ta ma’aikatan hukumar da wasu ɓangarori.

“Dukkanin ɓangarorin da muka zauna da su sun roƙe mu da mu jingine yajin aikin bisa tattaunawa kan nemo hanyoyin magance matsalolin da muke fuskanta, mun amince da jingine yajin aikin bisa girman su da muke gani, kuma za’a ci gaba da tattaunawa akai don neman mafita akai, “in ji Muntari”.

Tattarawa, ya kuma ce shugaban ƙungiyar ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano, ya buƙaci kowanne ma’aikaci da ya koma bakin aikin sa, domin ci gaba da gudanar da aiki.

Ya kuma ce za su koma teburin sulhu domin ci gaba da tattaunawa don neman nasarorin da ake nema, domin kamo bakin zare kan matsalolin da suke fuskanta.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano, suka tsunduma yajin aikin sai baba ta gani, kan gaza fara biyansu sabon tsarin albashi, da kuma karya wasu alƙawarurruka da suka yi da shugaban hukumar Injiniya Garba Ahmad Bichi, ko da dai ya musanta zarge-zargen da suka yi akan sa.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ba za mu dawo da ruwan sha ba a Kano, sai an sanya mu a sabon tsarin albashi – Ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha

Published

on

Ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano, sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani, bisa wasu dalilai da suka bayyana da ke damun su.

Shugaban ƙungiyar ƙwadago reshen hukumar samar da ruwan sha a jihar Kano Kwamared Najib Abdulsalam, shi ne ya sanar da hakan yayin zantawar sa da Dala FM a cikin daren yau Talata.

Kwamared Najib ya kuma ce ma’aikatan sun tsunduma yajin aikin sai baba-ta gani ɗin ne sakamakon yadda aka gaza biyan ma’aikatan ruwan sabon tsarin albashi na mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 71,000.

A watan Nuwamban shekarar nan ta 2024, ne dai gwamnatin jihar Kano ta fara biyan ma’aikatan jihar mafi ƙarancin albashin, ko da dai wasu ma’aikatan na ci gaba da kokawa kan rashin samun sabon tsarin albashin.

“Dukkanin ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha a jihar Kano babu wanda ya samu sabon tsarin albashi duk kuwa da yarjejeniyar da muka yi a baya, hakan ne ya sa muka tafi yajin aikin har sai an magance matsalar, “in ji Najib”.

Ya kuma ce sun kashe ruwan sha a jihar Kano, kuma ba za su dawo da shi ba har sai an biya ma’aikatan sabon tsarin albashin, da manajan daraktan Hukumar ya karya Yarjejeniyar da suka yi da shi.

Najib ya ƙara da cewar aikin ma’aikatan aiki ne mai matuƙar ban tausayi bisa yadda suke aiki a cikin ruwa cikin dare da rana, a don haka suke kira ga gwamnatin jihar Kano da ta kawo musu ɗauki wajen magance matsalar da suka fuskanta ta rashin biyan nasu sabon tsarin albashin.

Continue Reading

Trending