Connect with us

Labarai

Ko me ya jawo shugaban majalisa ya stige mataimakin sa?

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta amince da tsige mataimakin shugaban majalisar daga kan mukamin sa, Mukhtar Isaha Hazo, wanda ke wakiltar Basawa a karamar hukumar Sabongari, bisa zargin sa da hada baki da wasu daga cikin ‘yan majalisar 21 domin tsige shugaban majalisar, Yusuf Ibrahim Zailani wanda yake son maye gurbin sa a shugaban majalisar.

Rahotonni sun bayyana cewar yan majalisa 21 sun shirya da zarar sun zo majalisar za su kawo kudirin tsige shugaban majalisar, inda shi kuma shugaban majalisar da ya samu labari ya shirya zaman gaggawa a yau domin tsige mataimakin na sa.

Wakilin mu a jihar Kaduna, Babangida Aliyu Abdullahi ya rawaito cewa kafin tsige mataimakin shugaban majalisar da misalin karfe daya na rana kuma mambobin majalisar sun gudanar da wani zaman sirri a tsakanin su.

Zaman majalisar ya samu halartar ‘yan majalisa 25 inda su ka amince da a tsige mataimakin shugaban majalisar bisa aikata zamba cikin aminci da cin amana da a ke zargin sa da yi.

Kafin zauran majalisar ya amince da cire mataimakin shugaban majalisar an samu rikici tsakanin mambobin inda wasu su ka amince da a tsige shi wasu kuma su ka nuna rashin goyon bayan su.

Yayin zaman a yau tubabben mataimakin shugaban majalisar, Mukhtar Isah Hazo ya yi kokarin sace sandan majalisar wanda wasu daga cikin ‘yan majalisar su ka dakatar da yunkurin na sa na fita da sandan majalisar.

Yanzu haka dai ta tabbata Mukhtar Isah Hazo ya rasa kujerar sa ta mataimakin shugaban majalisar inda zai ci gaba da wakilitar karamar hukumar sa da yake wakilta ta Basawa dake Sabon Gari a jihar ta Kaduna.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending