Connect with us

Labarai

Hukumar Hisba ta fasa giya na makudan milyoyi- Ibni Sina

Published

on

Hukumar Hisba a jihar Kano ta fasa kwalaben giya da kudin ta ya kai kimanin naira milyan dari biyu da hamsin.

Shugaban hukumar Sheikh Harun Ibni Sina ne ya bayyana hakan yau Litinin, a shelkwatar hukumar dake sharada, bayan dawo wa daga sansanin fashen giyar.

Ya na mai cewa, “Shekarar 2004 ne a ka samar da dokar shigowa da giya, raba wa da tace wa, har ma da shan ta, haramun ne. Sannan kuma mataki na biyu kama giyar, mataki na uku neman izini daga kotu domin fashe giyar da aka kama, matakin karshe sahalewar gwamnan jihar Kano domin fasawa”. A cewar Sheikh Harun.

Ibni Sina ya kara da cewa, “Manzon Allah (S.A.W) ya yi tsinuwa a cikin giya, ya tsinewa mutane goma a kan giya, to mutum ya zai yi da wanda annabi ya tsinewa akan giya, saboda haka mu a wurin mu nasara ce, kuma ba yanzu a ka fara ba, hatta zamanin manzon Allah (S.A.W) an yi fashen giya”. Inji Harun Ibni Sina.

Ya kuma ce, “Ba mu gama fashen giyar ba za mu ci gaba da yi, ina godiya da gwamnan jihar Kano, dama sauran jami’an tsaron da su ka bayar da gudunmawa wajen fashen giyar”.

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Soron Dinki ya rawaito cewa, Sheikh Harun IbNI Sina, sun yabawa al’ummar gari akan hadin kan da suke bayarwa domin dakile shigo da giya jihar Kano.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Mu godewa Allah a kan jarabawar da ya dora mana – Limamin Madina

Published

on

Limamin masallacin Madina Sheikh Aliyu Abdul Rahman Al Hudaifyi ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su rungumi dabi’ar yin hakuri duba da yadda Allah ke jarrabar su da ibtila’i daban-daban.

Sheikh Hudaifyi ya bayyana hakan ne ta cikin hudubar juma’a dake zuwa kai tsaye a tashar Dala wanda Malama Maryam Abubakar take fassara wa.

Ya ce” Kamata al’ummar musulmi su rinka yin godiya ga Ubangiji a dukkanin jarrabawar da Allah ya jarrabe su da ita, duk mutumin da yake hakuri to Allah zai ba shi lada mai yawa”.

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewa Sheikh Aliyu na cewa ya kamata mutane su dage da addu’o’in samun sauki a dukkannin al’amuran rayuwa.

Continue Reading

Labarai

Tun da ba zuwa aikin Hajji ku taimakawa masu da’awa – Liman

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Ihya’us Sunnah da ke kofar Nasarawa, Malam Anas Abbas Ibrahim ya ce, Tun da a bana ba a samu damar zuwa aikin Hajji da Umara ba, kamata ya yi masu hali su tallafawa kungioyi da kuma al’ummar da su ke fita wa’azi na musuluntar da wadanda su ke ba musulmai ba.

Malam Anas Abbas Ibrahim ya bayyana hakan ne a hudubar da ya gudanar a Juma’ar nan.

Ya ce, “Manzon Allah (S.W.A) an taba hana shi ya yi aikin Umara, wanda hakan ya jawo a ka yi sulhu  a Hudaibiya, bayan anyi sulhun ya hakura, daga nan shi da Sahabban sa su ka himmatu domin jawo mutane su shigo musulunci, manzon Allah (S.W.A) da kan sa ya rubuta wasiku ya aikawa sarakunan duniya, kamar sarkin Farisa da kuma sarkin Rum”.

Malam Anas ya kara da cewa, “A shekarar da a ka yi sulhun ne kuma wadanda su ka shiga musuluncin sun ninka wadanda su ka shiga gabanin haka”. A cewar Malam Anas Abbas

Wakilin mu Tijjani Adamu ya rawaito cewa, Malam Anas ya kuma ja hankalin samarin da su ke hawa dandalin sada zumunta, su yi kokarin yada abubuwa kyayawa na musulunci tare da kiran mutane zuwa musulunci.

 

Continue Reading

Labarai

Iyaye su dora ‘ya’yan su a kan koyarwar addini

Published

on

Limamin masallacin juma’a na unguwar Kabuga ‘Yan Azara, Malam Abubakar Shua’aibu Dorayi ya ce, iyaye su rinka bibiyar alkur’ani da hadisi domin tsinto misalai da hanyoyin tarbiyar ‘ya’yan su.

Limamin ya bayyana hakan ne a hudubar da ya gudanar a masallacin a Juma’ar nan.

Ya na mai cewa, “Annabi ya hore mu a duk lokacin da za mu yi aure mu auri mai tarbiya. Idan kuma yaro ya girma a saba masa da ambaton Allah, tare da nuna masa abun da Allah yake so da wanda baya so, wannan zai sa ya tashi ya na girmama umarni da hanin manzon Allah, kuma a koya masa kadaita Allah”. Inji Malam Abubakar Dorayi.

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Soron Dinki ya rawaito cewa, limamin ya kuma ja hankalin iyaye da su zamo makarantar ‘ya’yan su a gida, wajen koya mu su addu’a a duk abun da za su gudanar.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish