Labarai
Leda uku ta ruwa ta farfado da wata mata da a ka rataye
Ana zargin wasu makwabtan wata mata Marfu’a Mukhtar da rataye ta ranar Asabar din makon da ya gaba ta a unguwar Bubbugaje gidan Jakada dake kamar hukumar Kumbotso.
Al’amarin ya faru ne da misalin karfe goman daren ranar, inda aka yi zargin mutanen guda biyar mata biyu da maza uku sun shiga gidan matar, su ka kuma yi amfani da igiyar guga wajen rataye ta a tagar dakin ta.
Bayan an kai ta asibiti tasha ledan ruwa uku ta farfado farfado, Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya zanta da ita tana mai cewa, “Makwabta na ne guda biyu da muke rigima da su, suka zo su ka kwankwasa min kofa su ka ce sun zo mu yi sulhu, ina bude kofa matan biyu suka shigo tare da maza guda uku, matan suka yi dariya suka fita, mijin kwabciyar tawa ne ya bani waya ta ya ce, in kira ‘yan uwana su ceto ni, tunda kome zan yi sai na kira waya, shi ne na kira Abdullahi abokin mijina, sai suka yanki igiyar guga suka nada min a wuya suka rataye min wuya har na fita daga hayyacina. Ni dai abin da nake bukata shi ne mahukunta su bi min hakkina”. A cewar Marfu’a.
Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Soron dinki ya zanta da mahaifin Marfu’a, Malam Mukhtar Muhammad dake Dorayi Chiranci, inda Ya ce, “Lokacin da abin ya faru wajen karfe goma na dare aka bugo min waya aka ce Marfu’a an rataye ta, gaba daya hankalin mu ya tashi, shi ne na tura wasu su je, saboda matasa sun tafi da makamai, kada su bari yaran su sari kowa, domin kada a bari su dauki doka a hannu, kuma ana zuwa aka ga an rataye ta. Inji Malam Mukhtar.
Kazalika, mijin Marfu’a Sani Isma’il Ya ce, “Na bar cajin waya ta mata ta ta kira wayar ta ba ta samu ba, sai ta kira lambar abokina, sai makwabtan nawa suka afka mata, kuma ko a ofishin ‘yan sanda sun yi barazanar sai sun kashe ni kuma bamu san abin da mu ka yi mu su ba”. A cewar Sani Isma’il.
Shi ma wanda ya ceto Marfu’a, Abudllahi Muhammad Wada, ya magantu da cewa, “Ni ne farkon wanda na fara zuwa gidan nata, da ta kira ni na daga wayar, sai naji an kwace wayar, na kira mijin bai daga ba, ina zuwa na shiga naga an rataye ta, sai na dauke ta a hoto saboda shaida.” Inji Abdullahi Muhammadu.
Wakilin mu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, mun yi kokarin jin ta bakin wadanda ake zargi amma basu magantu ba, saboda suna hannun ‘yan sanda, inda kuma Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta wayar hannu ya shaida cewar sun samu labarin faruwar al’amarin amma bai yi martani ba.
Labarai
Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya naɗa Ɗan Sa a matsayin Chiroman Kano.
Mai martaba sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya buƙaci dukkanin hakimansa da ke faɗin jihar nan da su mayar da hankali wajen gudanar da aikin su bisa gaskiya da riƙon Amana.
Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, kuma babban ɗan fadar Sarki, yau Juma’a a fadar sa.
Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, ne bisa cancanta da zuminci da kuma gogewarsa akan aikinsa na ƴan sanda, tare kuma da taimakawa al’umma da yake yi a koda yaushe.
Mai martaba sarkin ya kuma taya Chiroman Kano, murna bisa wannan naɗin da aka yi masa, tare da fatan zai zamo jakada na gari musamman wajen samar da cigaban Al’umma da kuma masarautar Kano.
Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa taron naɗin ya samu halartar gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da sarakunan gargajiya daga wasu daga cikin jahohin ƙasar nan.
Labarai
Za mu magance matsalolin da hukumar Hisbah ta Dala ke fuskanta – Shugaban ƙaramar hukumar Dala
Ƙaramar hukumar Dala ta ce za ta yi bakin ƙoƙarin ta wajen magance matsalolin da hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala ke fuskanta, domin ƙara ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukan al’umma.
Shugaban ƙaramar hukumar Suraj Ibrahim Imam ne ya bayyana hakan, a lokacin da jami’an hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala, suka ziyarce shi a ofishinsa, domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da suka yi, tare da sanar dashi halin da hukumar Hisbar ke ciki a halin yanzu.
“Daga cikin ƙalubalen da zan yi ƙoƙarin magance wa akwai samar da ruwa da wutar lantarki da kuma samar wa hukumar kayan aiki, bisa yadda suke fama da rashin su, “in ji Suraj Imam”.
Shugaban ƙaramar hukumar ta Dala Sura ya kuma yi kira ga babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da ya ƙara kulawa da walwalar hukumar ta ƙaramar hukumar Dala bisa ƙalubalen da suke fuskanta.
Da yake nasa jawabin kwamandan hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala Mallam Umar Bala Muhammad, ya ce sun ziyarci shugaban ƙaramar hukumar ne domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da kuma sanar da shi halin da hukumar ke ciki, domin haɗa ƙari da ƙarfe wajen magance ƙalubalen da suke fuskanta.
Wakiliyarmu Hadiza Balanti ta rawaito cewa Mallam Umar Bala ya kuma ƙara da cewa a shirye hukumar hisbar ta ƙaramar hukumar Dala take wajen gudanar da ayyukan al’umma babu gajiyawa.
Labarai
Mun dakatar da karɓar kuɗin haraji a Fagge har sai an kammala bincike – Shugaban Ƙaramar hukumar Fagge
Ƙaramar hukumar Fagge ta dakatar da dukkannin harkokin karɓar haraji har zuwa lokacin da za’a kammala bincike, don tabbatar da cewa bangaren harajin nayin aiki bisa doka domin ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Shugaban ƙaramar hukumar ta Fagge Salisu Usman Masu ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da tashar Dala FM Kano, a safiyar yau Talata.
Salisu Usman ya kuma bayyana cewar duk filotan da aka yanka aka sayar ko aka bayar ba bisa ƙa’ida ba shima an soki shi.
Shugaban ya kuma yi kira ga ƴan kwangila waɗanda suka watsar da ayyukan da aka basu da su dawo bakin aiki ka’in da na’in.
A cewar sa, “Na fahimci irin kalubalen da ke damun al’umma a ɓangaren lafiya a ƙaramar hukumar mu ta Fagge; kuma za mu yi ƙoƙarin samar da kayan aiki domin magance matsalar, “in ji shi”.
Masu ya kuma bayyana cewar ƙaramar hukumar ta Fagge za ta inganta harkar ilimi da tsaro, da Lafiya, inda kuma yi kira ga duk wani mai kaunar ci gaban karamar hukumar Fagge da ya taho a hada hannu ko da shawara zai bayar dan ciyar da karamar hukumar gaba.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su