Manyan Labarai
Magoya bayan Liverpool ku jinkirta da murna haka -Klopp
Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya gargadi magoya bayan kungiyar da su dakata daga murnar da su ke aiwatar wa a birnin Liverpool har sai lokacin yin murnar ya karaso.
Mai horaswar na furta hakan ne biyo bayan da duban magoya bayan kungiyar ke aiwatar da murnar lashe gasar a karo na farko tun cikin shekaru 30 ba su dauki gasar Firimiya ba, wanda duban magoya baya su ke aiwatar da murnar lashe gasar.
Ya ce”Ni kamar yadda ku ke murna a ranku ni ma haka nake cike da ita, amma ba a wannan lokacin ba, sakamakon wannan halin da a ke ciki. Saboda yin murnar zai mayar da hannun agogo baya idan mu ka duba za mu yada wannan cutar ne ta Corona kuma ba bukatar yada cutar a cikin al’umma, mu yi hakuri mu yi murnar, amma mu kiyaye gudun yin cinkoso”. Klopp
Yanzu haka Liverpool na da maki 86 a cikin wasanni 31 da ta fafata a gasar ta bana.
Manyan Labarai
Sulhu da ƴan Bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba – Human Rights
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta ƙasa da ƙasa wato International Human Rights Commission, ta ce sulhu da ƴan bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a ƙasar nan.
Babban daraktan ƙungiyar Kyaftin Abdullahi Bakoji Adamu mai ritaya, shi ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano.
Ya ce kasancewar ƴan bindigar basu da wata manufa bai kamata ayi sulhu da su ba, mai-makon hakan yafi dacewa a rinƙa ɗaukar tsauttsauran mataki akan su duba da yadda suke cutar da al’umma.
Ya kuma ce batun da mai bai wa shugaban ƙasa akan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribaɗo, ya yi a baya baya nan, kam cewar an fara samun fashimtar juna da wasu daga cikin ƴan Bindigar da suka addabi mutane a sassan ƙasar nan, a wani ɓangare ma kama da yin sulhu da su, ya faɗi hakan ne kawai amma hakan ba zai haifar da Ɗa mai ido ba.
Manyan Labarai
Gwamnatin Kano ta kulle wata makaranta mai zaman kan ta a jihar
Gwamnatin jihar Kano ta rufe wata makaranta mai suna Golden Crown International School a jihar, da ke yankin Sabon gari, bisa zargin an fake da sunan makarantar ana haɗa magani mara inganci mai-makon koyar da karatu a ciki.
Shugaban kwamitin yaki da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya na jihar Kano General Gambo Mai Aduwa Mai ritaya, ne ya bayyana hakan, a lokacin da Kwamitin ya kai wani sumame da karfe uku da rabi na daren jiya Talata.
Rahotanni sun bayyana cewa makarantar tana kan titin Zungero da ke cikin ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano, wanda bayan samun bayanan sirri aka ɗauki matakin kulle ta.
Mai Aduwa, ya ƙara da cewar tsarin gurin ta waje ya nuna makaranta ce amma kuma sai ake sarrafa magani da ake zargin ingancin sa da bai kai yadda ya kamata ba, tare da ajiye Allurai da kayan haɗa magani cikin ajujuwan mai-makon ɗalibai.
“Za mu faɗaɗa bincike akan al’amarin dan sanin matakin da za mu ɗauka na gaba, “in ji shi”.
Suma masu gadin gurin da muka zanta da su sun bayana cewar, aikin gadi kawai suke yi amma basu da masaniyar abubuwan dake gudana a cikin makarantar, da ake zargin ana sarrafa magani mara ingani da ajiye shi a muhalin da ake zargin bai yi dai-dai da tsarin doka ba.
Wakilinmu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewa shugaban kwamitin ya ce, zai ci gaba da bibiyar guraren dake yin abubuwan da za su kawo koma baya ga harkokin lafiya, da ci gaban jihar Kano, musmman wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya.
Manyan Labarai
Ƙaramar hukumar Tofa ta musanta zargin gididdiba burtalai a wasu garuruwan ta uku
Ƙaramar hukumar Tofa ta musanta batun gididdiba burtalai a garuruwan Yanoko da Gajida da kuma Dindere, dukka a ƙaramar hukumar da ake zargin an siyarwa Manoma, domin suyi aikin Noma.
Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar ta Tofa Abubakar Sulaiman Mai Rogo, ne ya bayyana hakan a daren jiya Laraba, lokacin da yake tsokaci kan koken da Fulani Makiyaya mazauna garuruwan suka yi, kan yadda suka zargi an gididdiba burtalai a yankunan su, an siyarwa wasu Manoma, domin suyi aikin Noma, lamarin da suka ce hakan barazana ce a gare su.
Mai Rogo, ya kuma ce ƙaramar hukumar ba ta da hannu wajen gididdiba burtalai a garuruwan, yana mai cewa ko da kansilolinsa daga zuwan su bai taɓa sanin wanda ya siyar da koda kuwa kunya ɗaya ba a cikin shugabancin sa na ƙaramar hukumar domin ayi Noma, haka shima bai siyar ba.
“Yanzu haka ana kan ɗaukar matakin doka akan waɗanda suka fitar da al’amarin, kasancewar maganar tana wajen ƴan sanda, kuma ana faɗaɗa bincike, “in ji shi”.
A ziyarar gani da Ido, da tashar Dala FM Kano, ta kai wasu daga cikin burtalan da aka yi zargin an siyarwa Manoman, ta iske yadda wasu mutane suke share guraren, kamar yadda suka shaida cewa waɗanda aka siyarwa ne suka basu aikin share wajen.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, wannan na zuwa ne bayan da wasu Fulani Makiyaya mazauna garuruwan suka koka, bisa yadda suka ce an gididdiba burtalai a yankunan su, duk da wani manomi yace har takarda aka bashi bayan an siyar masa, lamarin da ya sa su cikin damuwa bisa yadda hakan ka iya sanyawa su rasa guraren da za su yi kiwon Shanun su.
-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su