Connect with us

Labarai

Shekara guda: Ina a ka kwana a batun gidauniyar Umar Sa’idu Tudun Wada?

Published

on

Shugaban kungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen jihar Kano, Kwamrade Abbas Ibrahim, ya ce har yanzu kungiyar na yunkurin kafa gidauniya mai suna Umar Sa’id Tudun Wada, wadda za ta tallafawa iyalan sa.

Kwamrade Abbas Ibrahim na wannan batun ne a wajen taron addu’ar shekara guda da rasuwar Umar Sa’id Tudun Wada da kuma tunawa da shi wanda ya gudana yau Talata a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnatin Kano.

Ya ce” In Allah ya yarda mu na yunkurin kafa gidauniya mai suna UST, domin tallafawa  iyalan sa mu na kan wannan batun wajen ganin wannan gidauniyar ta tabbata”. A cewar Kwamrade Abbas.

Lokacin da marigayin UST ke jawabi a wajen taro.

Marigayin ya rike mukamaki a wasu daga cikin kafafen gidajen rediyo a Kano ciki akwai Freedom Radio wanda ya rike mukamin Janar Manaja da mataimakin shugaban rukunin tashar Freedon rediyo, ya yi Manajan Darakta na rediyo Kano da kuma Daraktan yada labarai na gidan gwamnatin Kano lokacin tsohon gwamnan Kano Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya kuma yi aiki a sashen hausa na rediyo Amurka.

Yayin da marigayin ke aiki a sashen Hausa na Rediyo Amurka.

Marigayi Umar Sa’id Tudun Wada wanda ya samu lakabin UST, kafin rasuwar sa ya bada gudunmawa a bangaren aikin jarida ciki da wajen jihar Kano da kasa da kuma duniya baki daya. Wanda ya tallafa wajen yin amfani da ilimin sa na koyarwa da fadakarwa tare da sa wasu daga cikin ma su aikin jarida a kan hanya. Sannan a duk lokacin da aikin zabe ya taso marigayin ya kan yi iya kokarin san a bada gudunmawa ga wadanda za su yi aikin wajen koyar da su yadda za su yi aikin tare da kare kan su a yayin aikin. Sannan a duk ranar Laraba a kan gayya ce shi zuwa makarantar koyar da ‘yan jarida wanda tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya bude a gidan talabijin din ARTV wato Kano Development Journlism Institute domin nunawa dalibai ma’aikata ilimi a kan aikin jarida.

 

Marigayin na jawabi a wajen taro.

Haka zalika an sanyawa sabon masallacin juma’a na rediyon manoma dake unguwar Tukuntawa a karamar hukumar birni mai suna Umar Sa’id Tudun Wada, sakamakon gudunmawa da ya bayar wajen yada addinin musulunci kasancewar shi ne mutumin da ya assasa harsashin ginin masallacin lokacin ya na shugaban gidan rediyon Kano kafin rasuwar sa.

Marigayi Umar Sa’id Tudun Wada na zaune a ofishin sa kafin rasuwar sa.

Marigayin ya rasu ne a lokacin da yake dawo wa daga kan hanyar sa ta Abuja zuwa garin Kano, inda ya gamu da hadari a kan hanyar sa ta dawo wa Kano daga Kaduna. Ya kuma bar mata Uku da kuma ‘ya’ya da dama tare da jikoki.

Lokacin da UST ke gabatar da shiri a wajen aikin sa kafin rasuwa.

A yayin taron wanda wakilin mu Abubakar Sabo ya halarci taron addu’o’in marigayi UST tare da tunawa da shi, ya ce mutane da dama ne su ka halarci taron daga sassan jihohin kasar nan ciki harda jihar Kano, sannan yayan marigayin Alhaji Yakubu Sa’id Tudun Wada da kuma shugabar taron Sa’a Ibrahim wadda ita ce shugabar tashar ARTV, sai shugabar kungiyar ‘yan jarida mata Bilkisu Ado Zango tare da Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Kwamrade Muhammad Garba.

Labarai

Shugabanni ku fito da sabbin dabaru domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta tsadar rayuwa a ƙasa – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights dake jihar Kano, ta ce akwai buƙatar shugabanni suyi abinda ya dace dan ganin an kawo karshen matsalar tsaro, da kuma ta harkar tsaro dake ci gaba da addabar mutane a sassa ƙasar nan.

Daraktan ƙungiyar Kwamared Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantwarsa da gidan rediyon Dala FM, a ranar Laraba, ya ce yadda ake ƙara samun ƴan ta’adda suna sace mutane tare da kashe su a sassan ƙasar nan, da kuma halin matsin rayuwar da ake fuskanta akwai buƙatar shugabanni suyi abinda ya kamata dan ganin an kawo ƙarshen matsalolin.

“Yawaitar kai hare-haren da ake samu daga ɓangaren ƴan bindiga a cikin al’ummar gari akan kashe su tare da sace su matuƙar ana son a kawo karshen matsalar, sai an ƙara himma wajen samar da makamai ga jami’an tsaro tare da samar da sabbin dabaru domin kawar da matsalar, “in ji Galadanci”.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kaɗan da sako ɗalibai aƙalla su sama da 285, na makarantar Kuriga dake ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, da ƴan bindiga suka sace su a baya, baya ga wasu ɗaliban da aka sace a wata makarantar Tsangaya a jihar ta Kaduna, wanda ko a jihar Borno ma aka jiyo yadda aka sace ƴan gudun hijira da dama a baya-bayan nan, inda matsalolin tsaron ke ƙara yin gaba a sassan ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnan Kano ya kafa kwamitin duba yadda ake rabon tallafin abincin Azumi

Published

on

Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin duba yadda ake ciyarwar azumin watan Ramadan, a kananan hokumomin cikin birnin jihar 8, domin sa ido da duba yadda ake gudanar da aikin dafawa da rabawa al’umma abincin.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamitin ne ƙarƙashin kulawar mataimakin gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da wasu ƴan kwamitin.

Hakan na zuwa ne dai bayan da gwamna Abba Kabir, ya ziyarci wasu daga cikin wuraren da ake dafa abincin, inda ya nuna rashin jin daɗin sa kan yadda ya ga aikin ke gudana a karamar hukumar kumbotso.

Bayanin hakan ya fito ne ta cikin wata sanarwar da babban mai taimakawa gwamnan Kano, na musamman akan gidajen rediyo Bashir Aminu Fanshekara, ya aikowa manema labarai, ya ce an bayyana Alhaji Danyaro Yakasai, a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin mai mambobi 7.

Fanshekara ya ce kwamitin ya fara zagayawa wasu daga cikin mazaɓu dake karamar hukumar kumbotso, domin duba yadda ake dafawa da kuma raba abincin tallafin ga al’umma, inda suka suka fara da mazaɓar Na’ibawa a ranar Asabar 23 ga watan Maris ɗin shekarar 2024.

Continue Reading

Ilimi

Kaduna:- Daliban Kuriga sun sha ki iskar ‘yanci

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da rahoton cewa an sako duka ɗaliban makarantar Kuriga da ƴanbindiga suka sace.

 

An sace ɗaliban firamare da na sakandare su kusan 287 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna fiye da makonni biyu da suka wuce.

 

Sanarwar da gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya fitar ta ce an sako duka ɗaliban kuma suna cikin koshin lafiya.

 

Sanarwar ba tayi karin bayani ba game da irin matakan da aka bi wajen sako ɗaliban, sai dai gwamna Uba Sani ya nuna godiya ga shugaba Tinubu da mai bashi shawara kan tsaro da kuma sojojin Najeriya saboda irin rawar da suka taka wajen ganin an sako ɗaliban.

 

“Ba dare babu rana ina tattaunawa da Malam Nuhu Ribadu domin lalubo hanyoyin da za a bi wajen kubutar da daliban, kafin mu samu nasara,” in ji Uba Sani.

 

Galibinsu ɗaliban da aka sace ƴan shekaru biyar ne zuwa 18.

Continue Reading

Trending