Connect with us

Manyan Labarai

Relegation: Norwich City ta fada ajin ‘yan dagaji

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Norwich City ta tsunduma zuwa ajin rukunin ‘yan dagaji na Championship bayan da West Ham ta lallasa ta da ci 4-0.

A karo na farko a gasar Firimiya ta bana da a ka samu kungiyar farko da ta fara nitsewa daga cikin gasar bayan da take mataki na karshe a jadawalin jerin teburin gasar da maki 21 a cikin wasanni 35 da ta yi.

Yanzu haka wasa 3 ne ya rage a karkare gasar yayin da kungiyar Bournmouth ke tsaka me wuya ita da Aston Villa inda su ke da maki 27 da kuma 28 a gasar.

Manyan Labarai

Kotu ta bada umarni ga jami’an tsaro da hukumar Hisbah kan su dakatar da kama Mansura Isah

Published

on

Babbar kotun tarayya karkashin jagorancin mai Shari’a Abdullahi Liman, ta takadar da hukumar Hisba da kwamishinan ƴan sanda da kuma mataimakin babban Sifeton ƴan sandan kasar nan daga kama Mansura Isa.

Mai Shari’a Liman ya ayyana cewar ya yi hani ga waɗanda akayi karar ko ƴan korensu ko wakilansu, ko kuma wasu masu aiki amadadinsu daga kamawa ko tsorataswa ko gayyata har zuwa lokacin da za’a saurari kowane ɓangaren.

Wannan umarni dai ya samu ne a cikin wata ƙara mai lamba 159/2024, wadda Mansura Isah ta shigar tana karar hukumar Hisba da kwamishinan ƴan sandan jihar Kano.

Kotun ta sanya ranar 15 ga wannan watan dan sauraron kowane bangare a shari’ar.

Continue Reading

Manyan Labarai

Zamu farfaɗo da masana’antun ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano – Kwamishina

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta farfaɗo da masana’antun yin saƙa na ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar nan, domin samawa matasa aiki ta yadda za su dogara da kansu.

Kwamishinan ciniki da masana’antu na jihar Kano Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, ne ya bayyana hakan, yayin da ya ziyarci masana’antar saƙar kayayyaki ta ƙaramar hukumar Kura yau Laraba, domin duba halin da take ciki tare da duba yadda za’a farfaɗo da ita daga dogon suman da ta yi.

Tun dai a lokacin mulkin tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, a shekarar 2014, ne ya samar da injina a masana’antar, amma tsohuwar gwamnatin Kano da ta ganata ta yi watsi da masana’anatar.

Yayin duba masana’antar Kwamishinan cikinki da masana’antu na jihar Kano Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, ya kuma bada tabbacin farfaɗo da masana’antar yin saƙar ta ƙaramar hukumar Kura da ma na faɗin jihar nan, domin samawa matasa ayyukan yi.

Da yake yiwa Dala FM Kano, ƙarin bayani babban sakataren ma’aikatar ciniki da masana’antu na jihar Kano, Muhammad Yusuf Ɗan-duwa, ya ce, farfaɗo da masana’antar ta Kura, na zuwa ne bisa ƙokarin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da Kwamishinan ma’aikatar Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, domin samawa matasa ayyukan yi.

Ya kuma ce yadda tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta wofantar da masana’antar tsawon lokaci, a yanzu gwamnatin su za ta yi duk mai yiyuwa, domin ganin an ta ci gaba da aiki ka’in da na’in.

Tun dai a shekarar 2014 ne aka samar da injina a masana’antar, amma tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta wofantar da aikin, lamarin da ya sa aikin ya tsaya cak, inda gwamnatin Kano mai ci a yanzu ta ce za ta farfaɗo da ita domin samawa matasa aikin yi, da kuma bunƙasa tattalin arziƙi.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mun ware miliyoyin Kuɗi domin biyan ƴan Fansho haƙƙoƙin su – Gwamnan Kano

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatin sa ta ware Naira biliyan biyar domin biyan ƴan Fansho haƙƙoƙin su bisa la’akari da yadda ake samun matsala wajen biyan su kudaɗen su.

Gwamnan Kano ya yi wannan jawabin ne da safiyar yau Laraba, yayin taron majalisar zartarwa da gwamnatin jihar ta saba yi duk sati, domin tattauna batutuwan da suka shafi gwamnatin jihar Kano.

“Za mu tabbatar an biya dukkanin waɗanda suka dace hakkin su na Fansho, domin su samu damar gudanar da sana’o’in dogaro da kai da za su iya riƙe iyalan su, “in ji Gwamnan”.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamnatin Kano ta ce za ta tabbatar ta magance matsalar rashin ruwa da al’umma suke fuskanta a sassan jihar, domin samar musu da wani sauƙi.

Continue Reading

Trending