Connect with us

Labarai

Sarkin Kano ya sa baki a kan sauya mana Dagaci – Al’ummar Gera

Published

on

Al’ummar garin Gera da ke karamar hukumar Kumbotso su na korafi a kan yadda ake neman sauya musu dakacin da su ka zaba da wani mutum daban a garin.

Al’ummar garin sun yi korafin ne a ofishin kungiyar kare hakkin dan adam da jin kai ta kasa, Human Right Foundation of Nigeria a ranar Talata.

A zantawar gidan rediyon Dala da daya daga cikin al’ummar garin Adamu Gera a yayin gudanar da korafin na su.

Ya ce, “Korafin mu a kan zaben Dagacin Gera ne, Magajin Malam ya zo ya yi zabe tare da ‘yan sanda da ‘yan jarida a ka zabi Usman Garba, a ka ce saura nadi, mu ka je wajen sarki, martaba Aminu Ado, a ka ce mu je mu dawo, mun sake dawo wa yau a ka ce ba wannan maganar nadi, ashe wani bawan Allah ya na yaki da abin baya so. Muna mika koken mu ga sarki mai martaba ya duba ya taimaka mana, ana nema a murde mana wannan zabe”. Inji Adamu Gera

A nasa bangaren, shugaban kungiyar kare hakkin dan adam da jin kai, Alhaji Muhammad Bello Gadon Kaya ya ce, “Dama tun kwanaki sun zo sun kawo korafi, mun tura jami’an mu sun je sun yi bincike a cikin sirri, kamar yadda binciken mu ya nuna mutanen gari da sauran dakatai shi su ke so”. A cewar Muhammad Bello Gadon Kaya

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Soron dinki ya rawaito cewar, shugaban kungiyar ta kare hakkin Dan adam Muhammad Bello Gadan Kaya, ya kuma yi kira ga hakimin yankin da ya je ya jaddada al’amarin gaban sarki domin a yi adalci.

 

Labarai

Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya naɗa Ɗan Sa a matsayin Chiroman Kano.

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya buƙaci dukkanin hakimansa da ke faɗin jihar nan da su mayar da hankali wajen gudanar da aikin su bisa gaskiya da riƙon Amana.

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, kuma babban ɗan fadar Sarki, yau Juma’a a fadar sa.

Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, ne bisa cancanta da zuminci da kuma gogewarsa akan aikinsa na ƴan sanda, tare kuma da taimakawa al’umma da yake yi a koda yaushe.

Mai martaba sarkin ya kuma taya Chiroman Kano, murna bisa wannan naɗin da aka yi masa, tare da fatan zai zamo jakada na gari musamman wajen samar da cigaban Al’umma da kuma masarautar Kano.

Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa taron naɗin ya samu halartar gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da sarakunan gargajiya daga wasu daga cikin jahohin ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Za mu magance matsalolin da hukumar Hisbah ta Dala ke fuskanta – Shugaban ƙaramar hukumar Dala

Published

on

Ƙaramar hukumar Dala ta ce za ta yi bakin ƙoƙarin ta wajen magance matsalolin da hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala ke fuskanta, domin ƙara ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukan al’umma.

Shugaban ƙaramar hukumar Suraj Ibrahim Imam ne ya bayyana hakan, a lokacin da jami’an hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala, suka ziyarce shi a ofishinsa, domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da suka yi, tare da sanar dashi halin da hukumar Hisbar ke ciki a halin yanzu.

“Daga cikin ƙalubalen da zan yi ƙoƙarin magance wa akwai samar da ruwa da wutar lantarki da kuma samar wa hukumar kayan aiki, bisa yadda suke fama da rashin su, “in ji Suraj Imam”.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Dala Sura ya kuma yi kira ga babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da ya ƙara kulawa da walwalar hukumar ta ƙaramar hukumar Dala bisa ƙalubalen da suke fuskanta.

Da yake nasa jawabin kwamandan hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala Mallam Umar Bala Muhammad, ya ce sun ziyarci shugaban ƙaramar hukumar ne domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da kuma sanar da shi halin da hukumar ke ciki, domin haɗa ƙari da ƙarfe wajen magance ƙalubalen da suke fuskanta.

Wakiliyarmu Hadiza Balanti ta rawaito cewa Mallam Umar Bala ya kuma ƙara da cewa a shirye hukumar hisbar ta ƙaramar hukumar Dala take wajen gudanar da ayyukan al’umma babu gajiyawa.

Continue Reading

Labarai

Mun dakatar da karɓar kuɗin haraji a Fagge har sai an kammala bincike – Shugaban Ƙaramar hukumar Fagge

Published

on

Ƙaramar hukumar Fagge ta dakatar da dukkannin harkokin karɓar haraji har zuwa lokacin da za’a kammala bincike, don tabbatar da cewa bangaren harajin nayin aiki bisa doka domin ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Fagge Salisu Usman Masu ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da tashar Dala FM Kano, a safiyar yau Talata.

Salisu Usman ya kuma bayyana cewar duk filotan da aka yanka aka sayar ko aka bayar ba bisa ƙa’ida ba shima an soki shi.

Shugaban ya kuma yi kira ga ƴan kwangila waɗanda suka watsar da ayyukan da aka basu da su dawo bakin aiki ka’in da na’in.

A cewar sa, “Na fahimci irin kalubalen da ke damun al’umma a ɓangaren lafiya a ƙaramar hukumar mu ta Fagge; kuma za mu yi ƙoƙarin samar da kayan aiki domin magance matsalar, “in ji shi”.

Masu ya kuma bayyana cewar ƙaramar hukumar ta Fagge za ta inganta harkar ilimi da tsaro, da Lafiya, inda kuma yi kira ga duk wani mai kaunar ci gaban karamar hukumar Fagge da ya taho a hada hannu ko da shawara zai bayar dan ciyar da karamar hukumar gaba.

Continue Reading

Trending