Connect with us

Manyan Labarai

Championship: Wycombe ta dawo gasar tun cikin shekaru 133

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Wycombe Wanderers, Adebayo Akinfenwa, ya ce ya tattauna da mai horas da Liverpool Jurgen Klopp har ma ya mayar masa da amsar sa a shafin sada zumunta na watsapp.

A karo na farko Kenan kungiyar kwallon kafa ta Wycombe ta kai bantan ta zuwa gasar ajin ‘yan dagaji wato Championship tun cikin shekaru 133 ba ta je cikin gasar ba, bayan da ta samu nasara a ranar Litinin da ci 2-1 a hannun Oxford United a filin wasa na Wembley.

Gwarzon dan wasan kungiyar kuma magoyin bayan Liverpool Adebayo, wanda kwantiragin sa ya kare a wannan kakar ya shaidawa Sky Sports cewa” na ji dadi abun da a ke ganin kamar ba zai yu ba, sai gashi kuma ya tabbata, domin kuwa ga shi mun kai ga nasara, shekaru hudu da su ka wuce kun tattauna da ni yau gashi na zama mai nasara”.

Manta Sabo

Kotu ta hana duk wata kafar yada labarai yin labarin da ya shafi Auwalu Danladi Sankara da Taslim Baba Nabegu.

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 4 karkashin jagorancin mai Shari’a Usman Na Abba ta yi hani ga duk wasu Jami’an Ƴan sanda ko na duk wata hukuma ta daban daga gayyata ko tsangwama, ko kuma bincike ko kamawa, ta kowace siga ga kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa Auwalu Ɗanladi Sankara.

Wannan dai na zuwa ne bayan da kotu ta wanke Auwalu Sankara daga zargin mu’amala ko alaƙa da juna tsakanin mai ƙara da Taslim Baba Nabegu har zuwa lokacin sauraran ƙarar.

Kotun ta kuma amince da rokon da wani lauya mai suna Barrister I.C Ekpinovi ya yi amadadin mai kara Auwalu Danladi Sankara wanda ya yi karar Nasiru Buba.

Mai karar ta bakin lauyansa ya bayyana wa kotun rokonsa inda ya roki kotun da ta dakatar da wanda ake kara ko dai shi da kansa ko kuma ƴan korensa daga ci gaba da yaɗa wata magana wadda wata babbar kotun Shari’ar Muslunci da ke Kano ta rufe.

Mai Shari’a Usman Na Abba ya ayyana cewar ko dai wanda aka yi kara ko yan korensa ko kuma wasu wakilansa, da a dai na yaɗa waccan magana har zuwa lokacin da kotun za ta saurari kowanne ɓangare.

Kotun ta ayyana cewar ta yi hani ga duk wata kafa ta yada labarai ko dai Rediyo ko Talabijin, ko shafukan sada zumunta da kafar Intanet da duk wata kafa wadda take iya sadar da labarai, daga yaɗa labaran da suka shafi Auwalu Ɗanladi Sankara da Taslim Baba Nabegu.

A ranar Talata ne dai gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar Namadi ya bayyana mayar da Auwalu Ɗanladi Sankara muƙamin sa na Kwamishinan ayyuka na musamman a jihar, bayan da kotu ta wanke shi daga zargin da hukumar Hisbah ta Kano, ta yi masa kan zargin baɗala da wata matar aure.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa kotun ta kuma sanya ranar 28 ga wannan watan na Nuwamba dan sauraron kowane ɓangare akan shari’ar.

Continue Reading

Manyan Labarai

Zargin Baɗala: Kotu ta wanke Auwalu Sankara da Taslim Baba Nabegu a Kano.

Published

on

Babbar kotun Shari’ar Muslunci mai zaman ta a kofar kudu ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola, ta sallami dakataccen kwamishina a jihar Jigawa, Auwalu Ɗanladi Sankara da Taslim Baba Nabegu.

Tun da farko kotun ce ta tura ofishin ƴan Sanda Shiyya ta ɗaya da ke jihar Kano, wato Zone 1, domin mukaddashin babban sifetan yansanda ya binciki zargin da ake wa Auwalu Danladi da Taslim Baba Nabegu, sakamakon korafin da wani mutum Mai suna Nasiru Buba ya yi, wanda ya zargi Auwalun da cewar suna yin mu’amalar da bata dace ba.

Cikin ƙunshin takaddar da muƙaddashin babban sifetan ƴansanda ya tura wa kotun ya bayyana cewar, hukumar Hisbah ta yi azarɓaɓi akan batun, kuma ya umarce su da su rinƙa yin aiki a bisa tsarin doka.

A zaman kotun na yau mai Shari’a Sarki Yola ya ayyana cewar babu tuhuma akan waɗanda ake zargin sakamakon yadda ƴan sanda suka gudanar da bincike, inda suka ce sun samu cewar maganar Jita-jita ce kuma Shari’a bata karɓar jita-jita.

Har ila yau, ma’aikatar Shari’a ta jahar Kano ta bayyana cewar babu tuhuma akan waɗanda ake zargin sakamakon rashin gamsassun hujjoji.

Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ayyana cewar ya sallami Auwalu Danladi Sankara da Taslim Baba Nabegu nan take, kuma kotun ta umarci kowa ya zauna lafiya.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa, da yake jawabi lauyan wanda ake ƙara Barrister Saddam Sulaiman, ya ce dama maganar siyasa ce ta shigo cikin al’amarin.

Continue Reading

Manyan Labarai

Masu Garkuwa da mutanen da muka kama a dajin Ɗansoshiya sun rasu – Ƴan Sandan Kano

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce masu Garkuwa da mutane su biyun da ta kama a dajin Ɗansoshiya da ke kwanar Ɗangora a ƙaramar hukumar Ƙiru a jihar sun rasu.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan a shafin sa na sada zumunta a cikin daren Asabar 09 ga watan Nuwamban 2024.

Tun dai da safiyar Asabar ne rundunar ta ce ta cafke mutane biyun da ta ke zarginsu da shiga jihar Kano, domin yin garkuwa da mutane tare da neman kuɗin fansa.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa, an kama mutanen ne a garin Kwanar Dangora, kuma, suna hannun ‘yan sanda domin fadada bincike, ko da ike yanzu haka tuni suka riga mu gidan gaskiya.

Majiyar Dala FM Kano ta rawaito cewa SP Kiyawa ya kuma ƙara da cewa, yanzu ta’addancin satar mutane ba za ta yi tasiri a Jihar Kano ba da yardar Allah’.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan na Kano, ya kuma gode wa al’ummar jihar bisa addu’o’in da suke yi a kullum.

Tuni dai Kiyawa ya wallafa hotunan gawar mutanen biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a shafin sa na Facebook.

Continue Reading

Trending