Connect with us

Lafiya

Wata mata ta kubuta da kyar a wurin mai Adaidaita sahu

Published

on

Ana zargin wata mata da ta shiga baburin adaidaita sahu mai adaidaita sahun ya so guduwa da ita inda kuma ta kubuta dakyar.

A zantawar gidan rediyon Dala da wannan mata ta bayyana yadda almarin ya faru da ita.

Ta ce, “Mun hau adaidaita sahu daga Sabo titi Gidan Karkara za’a kai mu unguwar Kuntau, sai da muka zo Junction din da za’a shiga Jambulo sai na ce malam ka bi ta nan, sai ya ce shi ba zai bi ba akwai sakon da zai karba, mu na cikin tafiya sai ya kai mu can wani lungu a can cikin Rijiyar Zaki, ya ce wai kwan lantarki zai siya, bai fada ba sai da mu ka zo cikin wani layi a Rijiyar Zaki, layin da ban ma san sunan sa ba”.

Ta kara da cewa, “Sai na ce malam duk ga shaguna nan ka siya, sai ya ce, babu inda zai samu sai a can, da ya shigar da mu wani layi akwai wani kanti, ya ce ga kantin nan anan zai samu gulob din, kuma ya na ajiye mu layin tsit babu kowa, kuma bai shiga kantin ba sai ya mike cikin wani layi mai duhu, sai naga ya dauko waya, ya na waya daga nesa ina hango shi, sai na gan shi tare da wasu mutane guda biyu, sai Allah ya bani nasara ni da yara na muka fito da gudu, da kyar mu ka sha mu ka fito bakin titi, mu ka samu wata motar muka hau”. Inji matar

A nasa bangaren, mijin wannan mata, Adam Bashir Yakubu, shima yayi Karin bayani a kan yadda al’amari ya faru, “Akwai iyalina da su ka hau adaidaita sahu zai kawo su Kuntau, su na tafiya ba fitila a daidaita sahun, sun zo Kabuga ya ce zai biya Rjiyar Zaki ya sayi kwan lantarki. Ina so jama’a su kula iyali na da kyar su ka sha, idan adaidaita sahu babu fitila kada su hau”. A cewar Adam Bashir

Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito cewa, Adam Bashir ya kuma yi kira ga jamai’an tsaro a kan su tashi tsaye wajen al’amarin tafiya da adaidaita sahu babu fitila, domin miyagu sun fara amfani da hakan domin cimma burin su.

Lafiya

Likitocin da ke aiki da gwamnatin Kano sun jingine yajin aikin gargaɗin da suka fara

Published

on

Likitocin da suke aiki da gwamnatin jihar Kano (NAGGMDP), sun jingine yajin aikin gargaɗin da suka fara a ranar Talata 01 ga watan Oktoban 2024, biyo bayan wani zama da su ka yi da kwamitin da gwamnatin ta kafa.

Sakataren ƙungiyar Dakta Anas Idris Hassan Shanno ne ya bayyana hakan ga manema labarai, jim kaɗan bayan kammala zaman gaggawa da su ka yi da ƴaƴan ƙungiyar.

Dakta Anas ya kuma ce sun ɗauki matakin jingine yajin aikin ne zuwa ƙarshen watan nan na 10, Kamar yadda gwamnatin ta dauki alkawarin cewa za ta biya masu buƙatun su a lokacin.

Wakilinmu Abubakar Sabo ya ruwaito cewa ƙungiyar ta kuma buƙaci dukkanin likitocin da ke ƙarƙashin ta da su koma bakin aikin su.

Continue Reading

Lafiya

An ƙaddamar da aikin gwaje-gwajen lafiya da bayar da magani kyauta a Kano

Published

on

Ƙungiyar ma’aikatan lafiya da unguwar zoma ta ƙasa reshen asibitin Ƙashi na Dala a jihar Kano, ta ƙaddamar da aikin gwaje-gwajen lafiya da bayar da magani kyauta ga al’umma.

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan lafiya na asibitin Ƙashi na Dala, Kwamared Abubakar Muhammad Isah, ne ya bayyana hakan a wani ɓangaren na tunawa da bikin ranar ma’aikatan jinya ta Duniya, wanda a nan Kano za’a shafe mako guda ana gudanar wa a jihar Kano.

Kwamared Abubakar Muhammad, ya kuma ce sun zaɓi gwaje-gwajen lafiya da bayar da magani kyauta, domin saukakawa al’umma.

A cewar sa, “Mutane ku rinƙa zuwa Asibiti ana gwada lafiyar ku ba sai baku da lafiya za ku je gwaji ba domin mai lafiya shine yake neman magani dan ya yi rigakafi, amma da zarar cuta ta ci karfin mutum to lamarin ya yi munin gaske, “in ji shi”.

Wakilinmu Yusuf Nadabo ya ruwaito cewar kungiyar za ta kwashe mako guda tana gudanar da taruka dan wayar da kan al’umma a kan batun lafiya.

Continue Reading

Lafiya

Ku rinƙa ziyartar Asibiti ana muku gwaje-gwajen fitsari da Jini domin sanin halin da ƙodar ku take ciki – Likita

Published

on

An shawarci al’umma da su rinƙa ziyartar Asibiti akai akai wajen duba lafiyar su, ta hanyar yin gwaje-gwajen fitsari da jini domin sanin halin da kodar su ke ciki.

Dakta Muhajid Sunusi Rabi’u ne ya bayyyana hakan yayin ganawarsa da Dala FM, lokacin da suke aikin gwaje-gwajen fitsari da jini, kyauta a ɗaya daga cikin makarantu masu zaman kan su a nan Kano.

Dakta Mujaheed ya kuma ce sun gudanar da aikin ne a wani ɓangare na bikin ranar ƙoda ta Duniya, wadda aka ware duk ranar Alhamis ta mako na biyu na kowanne watan Maris domin gudanar da bikin ranar.

Continue Reading

Trending