Connect with us

Lafiya

Jigawa: An kama barawon Babura

Published

on

Wani matashi da ya kware wajen satar babura, a jihar Jigawa ya shiga hannun rundunar ‘yan jihar, a daidai lokacin da ya ke shan jibga a hannun wasu mutane lokacin da dubun sa ta cika.

Rundunar ta ‘yan sanda ta bayyana cewar, ko a baya ta karbi rahoton sace wani babur Roba-roba kirar Lifan a unguwar Yelwawa Dutse, bayan bincike su ka gano matashin ne barawon da ya saci baburin.

Matashin mai suna Muhammad Yahaya Auwal, dan asalin jihar Kano mai shekaru 22, ya amsa da bakin sa cewa, shi ne ya saci babur din dama wasu da dama.

Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa SP Abdu Jinjiri ya ce, “Matashin ya shaidawa jami’an hukumar mu cewa, ya na amfani da mukullai daban-daban wajen satar Baburan mutane”. Inji SP Abdu Jinjiri

Wakilin mu Muhammad Aminu Umar Shuwajo ya rawaito cewa, rundunar ta kuma ce, su na cigaba da bincike kan matashin da zarar sun kammala za su gurfanar da shi gaban kotu.

 

 

Lafiya

Likitocin da ke aiki da gwamnatin Kano sun jingine yajin aikin gargaɗin da suka fara

Published

on

Likitocin da suke aiki da gwamnatin jihar Kano (NAGGMDP), sun jingine yajin aikin gargaɗin da suka fara a ranar Talata 01 ga watan Oktoban 2024, biyo bayan wani zama da su ka yi da kwamitin da gwamnatin ta kafa.

Sakataren ƙungiyar Dakta Anas Idris Hassan Shanno ne ya bayyana hakan ga manema labarai, jim kaɗan bayan kammala zaman gaggawa da su ka yi da ƴaƴan ƙungiyar.

Dakta Anas ya kuma ce sun ɗauki matakin jingine yajin aikin ne zuwa ƙarshen watan nan na 10, Kamar yadda gwamnatin ta dauki alkawarin cewa za ta biya masu buƙatun su a lokacin.

Wakilinmu Abubakar Sabo ya ruwaito cewa ƙungiyar ta kuma buƙaci dukkanin likitocin da ke ƙarƙashin ta da su koma bakin aikin su.

Continue Reading

Lafiya

An ƙaddamar da aikin gwaje-gwajen lafiya da bayar da magani kyauta a Kano

Published

on

Ƙungiyar ma’aikatan lafiya da unguwar zoma ta ƙasa reshen asibitin Ƙashi na Dala a jihar Kano, ta ƙaddamar da aikin gwaje-gwajen lafiya da bayar da magani kyauta ga al’umma.

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan lafiya na asibitin Ƙashi na Dala, Kwamared Abubakar Muhammad Isah, ne ya bayyana hakan a wani ɓangaren na tunawa da bikin ranar ma’aikatan jinya ta Duniya, wanda a nan Kano za’a shafe mako guda ana gudanar wa a jihar Kano.

Kwamared Abubakar Muhammad, ya kuma ce sun zaɓi gwaje-gwajen lafiya da bayar da magani kyauta, domin saukakawa al’umma.

A cewar sa, “Mutane ku rinƙa zuwa Asibiti ana gwada lafiyar ku ba sai baku da lafiya za ku je gwaji ba domin mai lafiya shine yake neman magani dan ya yi rigakafi, amma da zarar cuta ta ci karfin mutum to lamarin ya yi munin gaske, “in ji shi”.

Wakilinmu Yusuf Nadabo ya ruwaito cewar kungiyar za ta kwashe mako guda tana gudanar da taruka dan wayar da kan al’umma a kan batun lafiya.

Continue Reading

Lafiya

Ku rinƙa ziyartar Asibiti ana muku gwaje-gwajen fitsari da Jini domin sanin halin da ƙodar ku take ciki – Likita

Published

on

An shawarci al’umma da su rinƙa ziyartar Asibiti akai akai wajen duba lafiyar su, ta hanyar yin gwaje-gwajen fitsari da jini domin sanin halin da kodar su ke ciki.

Dakta Muhajid Sunusi Rabi’u ne ya bayyyana hakan yayin ganawarsa da Dala FM, lokacin da suke aikin gwaje-gwajen fitsari da jini, kyauta a ɗaya daga cikin makarantu masu zaman kan su a nan Kano.

Dakta Mujaheed ya kuma ce sun gudanar da aikin ne a wani ɓangare na bikin ranar ƙoda ta Duniya, wadda aka ware duk ranar Alhamis ta mako na biyu na kowanne watan Maris domin gudanar da bikin ranar.

Continue Reading

Trending