Connect with us

Labarai

Mun samu nasarori a sulhun mu da ‘Yan bindiga – Gwamnan Zamfara

Published

on

Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawallen Maradun ya yi kira ga Shugaban kasa Muhammad Buhari da ya goyi bayan sulhu da mahara da kuma gwamnonin arewa maso yamma.

Gwamna Bello Matawallen Muradun, ya bayyana hakan ne yayin da Babban Sefeton ‘yan sanda na kasa, Muhammad Adamu Abubakar ya kai ziyara jihar ta Zamfara inda ya yi ganawar sirri da gwamnan a gidan gwamnati da ke Gusau babban birnin Jihar Zamfara.

Ya ce, “Mu a nan Zamfara mun samu nasarori da dama sakamakon sulhun da mu ka yi da su mahara, kuma idan har gwamnatin tarayya ta marawa shirin sulhu da muka kirkiro da shi ga makwabtan jahohin, Sakoto da Katsina da Nija da kuma Kaduna, zai kawo zaman lafiya a yankin”.

Gwamna Matawalen ya kara da cewa, “Tuni gwamnati na ta kafa matsuguni uku a yankunan ‘Yan Majalisar Datawa ga Fulani, wanda zai bunkasa rayuwar su, kuma matsugunin akwai makarantu da mashayar ruwa da asibitocin dabbobi da na al’umma da wuraren wasanni”. A cewar Gwamna Matawalle

A nasa jawabin, babba Sefeton ‘yan sandan Muhammad Adam ya ce, “Mun yi ma Zamfara dirar mikiya ne dan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, a kan harkar tsaron jihar da kuma Sarakuna”. Inji Babban Sefeton ‘yan sanda

Muhammad Adam, ya kuma roki Sarakuna da su taimaka masu wajen yaki da suke da ‘Yan ta’adda , domin ganin an kawo karshen ta’addanci a yankin.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending