Labarai
Yadda a ke soya naman Rakumi
Kasancewar sallah ta gabato hakan ya sanya hada-hadar kasuwancin dabbobi a birnin Kano da kewaye, sai dai kuma a bana rakuma sun fi yawa a kasuwannin dabbobin.
A shekarun baya al’ummar jihar Kano ba’a saba ganin suna yanka dabbar rakumin ba sai dai-dai inda a bana abun ya canja, wanda kuma wasu sun yadda a ke sarrafa naman rakumin wasu kuma ba su sani ba.
Wasu matan aure da su ka dade suna aikin sarrafa naman rakumin sun yiwa gidan rediyon Dala bayanin yadda suke gudanar da aikin da cewar, “gaskiya gara naman sa, shi rakumi ba shi da mai naman sa ya na saurin lalacewa. Bamu taba amfani da shi ba sai bara, naman sa ma ba dadi, gandar sa ma bata ajiyu wa rubewa take yi”.
Kazalika, itama wata mata ta ce, “Gaskiya da naman rakumi ya na da tauri, amma yanzu ba shi da wani tauri, shi dai wajen babbakar sa ne yanzu idan ka ajiye shi zai yi tsutsa. Shekaru biyu mu na amfani da shi… gaskiya wanda zai yi suya ya tabbatar zai soya naman sa sai ya ga y ayi kumfa, inda kuwa ya yi kamar na sa idan ya ajiye zai yi tsutsa”.
“Rakumi ya na da muhimmanci fiye da kowace dabba, idan ka duba za ka ga kamar Saniya za ta fishi nama, to amma ya fi Saniya, wuyan sa kawai a ka ba ka za ka sha mamaki, sai kayi kasko uku, kuma ya fi na Saniya dadi”. A cewar wata mata
Shima wani magidanci mai suna Malam Nura Sani da ya dade ya na amfani da naman rakumin ya ce, “Akwai fa’idar da rakumi ya ke da ita, duk abun da ya ke jikin sa magani ne, kuma za’a samu wadataccen nama kowa ya wadata, na kai shekara 15 ina yanka naman, tun daga Mandawari har Sharada ba na jin akwai mai yanka rakumi in bani ba”.
Ya kuma ce, “Kowanne nama idan ka ga ya yi tauri to bai sha ruwa ba… idan a ka yayyanka a ka zuba masa ruwa ya dafu ruwan ya kone, shi da kan sa idan ya na da maiko zai soya kan sa, kamar dambun nama haka yake da laushi. Inji Malam Nura
Wakilin mu Tijjani Adamu ya rawaito cewa, Malam Nura Sani ya kuma ce, yanzu mutane su na tambayar sa ya na gaya musu yanda a ke sarrafa naman rakumin.
Labarai
Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya naɗa Ɗan Sa a matsayin Chiroman Kano.
Mai martaba sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya buƙaci dukkanin hakimansa da ke faɗin jihar nan da su mayar da hankali wajen gudanar da aikin su bisa gaskiya da riƙon Amana.
Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, kuma babban ɗan fadar Sarki, yau Juma’a a fadar sa.
Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, ne bisa cancanta da zuminci da kuma gogewarsa akan aikinsa na ƴan sanda, tare kuma da taimakawa al’umma da yake yi a koda yaushe.
Mai martaba sarkin ya kuma taya Chiroman Kano, murna bisa wannan naɗin da aka yi masa, tare da fatan zai zamo jakada na gari musamman wajen samar da cigaban Al’umma da kuma masarautar Kano.
Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa taron naɗin ya samu halartar gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da sarakunan gargajiya daga wasu daga cikin jahohin ƙasar nan.
Labarai
Za mu magance matsalolin da hukumar Hisbah ta Dala ke fuskanta – Shugaban ƙaramar hukumar Dala
Ƙaramar hukumar Dala ta ce za ta yi bakin ƙoƙarin ta wajen magance matsalolin da hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala ke fuskanta, domin ƙara ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukan al’umma.
Shugaban ƙaramar hukumar Suraj Ibrahim Imam ne ya bayyana hakan, a lokacin da jami’an hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala, suka ziyarce shi a ofishinsa, domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da suka yi, tare da sanar dashi halin da hukumar Hisbar ke ciki a halin yanzu.
“Daga cikin ƙalubalen da zan yi ƙoƙarin magance wa akwai samar da ruwa da wutar lantarki da kuma samar wa hukumar kayan aiki, bisa yadda suke fama da rashin su, “in ji Suraj Imam”.
Shugaban ƙaramar hukumar ta Dala Sura ya kuma yi kira ga babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da ya ƙara kulawa da walwalar hukumar ta ƙaramar hukumar Dala bisa ƙalubalen da suke fuskanta.
Da yake nasa jawabin kwamandan hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala Mallam Umar Bala Muhammad, ya ce sun ziyarci shugaban ƙaramar hukumar ne domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da kuma sanar da shi halin da hukumar ke ciki, domin haɗa ƙari da ƙarfe wajen magance ƙalubalen da suke fuskanta.
Wakiliyarmu Hadiza Balanti ta rawaito cewa Mallam Umar Bala ya kuma ƙara da cewa a shirye hukumar hisbar ta ƙaramar hukumar Dala take wajen gudanar da ayyukan al’umma babu gajiyawa.
Labarai
Mun dakatar da karɓar kuɗin haraji a Fagge har sai an kammala bincike – Shugaban Ƙaramar hukumar Fagge
Ƙaramar hukumar Fagge ta dakatar da dukkannin harkokin karɓar haraji har zuwa lokacin da za’a kammala bincike, don tabbatar da cewa bangaren harajin nayin aiki bisa doka domin ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Shugaban ƙaramar hukumar ta Fagge Salisu Usman Masu ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da tashar Dala FM Kano, a safiyar yau Talata.
Salisu Usman ya kuma bayyana cewar duk filotan da aka yanka aka sayar ko aka bayar ba bisa ƙa’ida ba shima an soki shi.
Shugaban ya kuma yi kira ga ƴan kwangila waɗanda suka watsar da ayyukan da aka basu da su dawo bakin aiki ka’in da na’in.
A cewar sa, “Na fahimci irin kalubalen da ke damun al’umma a ɓangaren lafiya a ƙaramar hukumar mu ta Fagge; kuma za mu yi ƙoƙarin samar da kayan aiki domin magance matsalar, “in ji shi”.
Masu ya kuma bayyana cewar ƙaramar hukumar ta Fagge za ta inganta harkar ilimi da tsaro, da Lafiya, inda kuma yi kira ga duk wani mai kaunar ci gaban karamar hukumar Fagge da ya taho a hada hannu ko da shawara zai bayar dan ciyar da karamar hukumar gaba.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su