Connect with us

Labarai

Har yanzu ba’a ga yaron da ya fada kududdufi ba

Published

on

Wani yaro dan shekaru 6, mai suna Ammar Nafi’u, a na zargin ya fada kududdufi a unguwar Gidan kuka da ke Dorayi Karama a karamar Hukumar Gwale tsawon kwanaki uku kuma har yanzu ba’a gan shi ba.

Wani mutum mai suna Ashiru Magaji, da ke makwabtaka da kududdufin a zantawar sa gidan rediyon Dala a ranar Laraba.

Ya ce, “Sarkin ruwa ya zo, ya dauki wajen awanni biyu a cikin ruwan ya kuma yi iya bakin kokarin sa, amma bai gano yaron ba, ko shi kan sa da ya fito akwai alamun ya wahala, ya kuma shawarci iyayen yaran a kan ba lallai a iya ganin yaron a lokacin ba sai dai bayan kwanaki biyu idan gawar tayo sama”.

Kazalika, wani magidanci da ya kai dauki cikin ruwan domin lalubo yaron ya ce, “Na shiga ruwan amma bamu samu yaron ba, tun takwas na safe har karfe biyu na rana ba’a gan shi ba na hakura, mutane da dama sun shiga ba’a gan shi ba, ruwan akwai sanyi sosai”. A cewar magidancin

A nasa bangaren mahaifin yaron, Malam Nafi’u Garba Mandawari, ya bayyana cewar, “Mun je dubiya mun dawo a ka ce yaron ya fada ruwan… Mun samu Hukumar kashe gobara, sun zo kuma su na zargin babu yaron a ciki, amma ni na tabbatar yaron ya na ciki, domin yayan sa ya nuna inda yaron ya fada. Gashi an zo da injina a na zuke ruwan”. Inji mahaifin yaron

Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewar, al’ummar unguwar sun yi kira ga gwamnati a kan ta cike kududufin domin ya na barazana ga yaran unguwar.

 

Labarai

Ƙudurin gyaran dokar gudanarwar Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi ya tsallake karatu na ɗaya a majalisar dokokin Kano

Published

on

Ƙudurin gyaran dokar gudanarwar Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke jihar Kano, ya tsallake karatu na ɗaya a zauren majalisar dokokin jihar.

Ƙudurin ya kai wannan mataki ne yayin zaman majalisar na yau Laraba, ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore, bayan da akawun majalisar Alhaji Bashir Idris Ɗiso, ya gabatar da karatun na ɗaya.

Har ila yau, yayin zaman na yau, majalisar ta buƙaci gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ta tallafa wa wasu kanikawa da kafintoci bisa iftila’in gobarar da ta ƙone musu kaya na miliyoyin Naira, tare da asarar rayuka a kan titin Lawan Dambazau.

Majalisar ta buƙaci hakan ne biyo bayan ƙudurin gaggawa da wakilin ƙaramar hukumar Birni da kewaye Alhaji Sarki Aliyu Daneji ya gabatar.

Yayin gabatar da ƙuɗurin, ɗan majalisar ya nemi gwamnatin data tallafa wa waɗanda gobarar ta shafa domin rage musu raɗaɗin iftila’in.

Majalisar ta kuma bukaci gwamnatin da ta ɗaga darajar asibitin garin Gano, zuwa matakin babban asibiti domin ƙara inganta kiwon lafiya a yankin har ma da sauran yankuna, kamar yadda ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Shu’aibu Rabi’u ya buƙata.

Wakilinmu na majalisar Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito cewa, a dai zaman na yau Laraba, shi ma ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ƙaraye, Injiniya Ahmed Ibrahim, ya gabatar da ƙudurin neman gwamnatin Kano ta gina titi a hanyar da ta tashi daga mahaɗar titin zuwa sansanin horas da matasa ƴan hidimar ƙasa, ta bi ta Kurugu da Dederi har zuwa Yammedi duk a yankin ƙaramar hukumar Ƙaraye.

Continue Reading

Labarai

Gwamnan kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sauya shugaban hukumar tattara haraji na jihar

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗin Dakta Zaid Abubakar, a matsayin sabon shugaban hukumar tattara kuɗaɗen haraji ta jihar Kano, da kuma Kasim Ibrahim a matsayin babban daraktan hukumar.

Babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar da aka aikowa Dala FM Kano, a daren jiya Laraba.

Sanarwar ta ce, tsohon shugaban hukumar Alhaji Sani Abdulkadir Dambo, an mayar da shi ne a matsayin mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin zuba jari, wanda kuma sauye-sauyen za su fara aiki nan take.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur: Fadar shugaban ƙasa kiyi wani abu dan mutane su samu sauƙi – Ƙungiyar Nothern Concern Soliderity

Published

on

Yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar wahalar man fetur a ƙasar nan, ƙungiyar da ta damu da abubuwan da suka shafi arewacin ƙasar nan ta Northern Concern Soliderity, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi abinda ya dace dan ganin mutane sun samu wani sauƙi.

Babban jami’in gudanarwar ƙungiyar, kuma sakataren riƙo na zauren gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya, Kwamared Saddat Usman Maiyaƙi, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, lokacin da yake nuna takaici kan irin wahalar da al’ummar ƙasa suke sha wajen shan man Fetur a gidajen man.

Ya ce duba da halin matsin rayuwar da al’umma suka samu kansu a ciki, akwai buƙatar shugabanni da masu ruwa da tsaki su kawo ƙarshen wahalar man Fetur ɗin da aka fama da ita.

Kwamared Saddat Maiyaƙi, ya kuma haƙurƙurtar da al’ummar ƙasar nan kan halin ƙuncin rayuwar da suka samu kai a ciki, inda ya yi fatan komai ya zo karshe cikin ƙanƙanen lokaci.

Continue Reading

Trending