Connect with us

Manyan Labarai

Majalisar dokoki: Za mu duba kudirin dokar masarautun Kano

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta karbi kwafin takarda daga gwamnatin jihar, wadda take dauke da bukatar majalisar ta sake yin kudirin dokar masarautun Kano kwaskwarima, domin gwamnatin ta samu samar nada karin ma su nada sarki da wa su dakatai.

Takarda da a ka baiwa Akawun majalisar, za a duba bukatar dake cikin ta a zaman majalisar na gaba.

A wani ci gaban kuma, dan majalisar mai wakiltar Gezawa, Isyaku Ali Danja, ya gabatar da kudirin sake bukatar majalisar ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano data sake gina hanyar da ta taso daga Kwanar kara ta bi ta Kwasangwami zuwa Ranawa ya hada da Babawa ya ratsa ta Danmadanho dukkanin su a Karamar hukumar ta Gezawa, domin amfanin al’ummar wannan yankin.

Wakiliyar mu Khadija Ishaq Muhammad ta ruwaito cewa, shi ma Lawan Hussaini Chediyar ‘yan Gurasa mai wakiltar karamar hukumar Dala ya bukaci gwamnati da ta sabunta bututun magudanan ruwa dake Kurna Masallachi ya biyo ta babbar hanya zuwa yankin Fagge duka a Dala.

Labarai

Ma’aurata su guji daukar dabi’u a kafofin sada zumunta – Malam Kabiru

Published

on

Shugaban makarantar Markazul Tabligul Risalatul Islam Malam Kabiru Ghali Ibrahim ya ce, Yanayin rayuwar wasu ma’auratan ke janyo matsaloli a zaman takewar aure.

Malam kabiru Gali Ibrahim ya bayyana hakan ne a ganawar sa da gidan rediyon Dala a ranar Alhamis

Yana mai cewa, “Lokuta da dama wasu ma’auratan su na daukar wasu dabi’u ne a kafofin sada zumunta ba tare da tantance sahihancin abin ba kuma suce za su gwada a gidajen su”.

Ya kuma ce, “Rashin sanya tsoron Allah a wajen neman aure na taka muhimmiyar rawa wajen samar da matsaloli bayan aure”. Inji Malam Kabiru.

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewar, Malam Kabiru Ghali Ibrahim ya kuma ja hankalin ma’aurata dama waɗanda ke da niyyar auren kan su sa tsoron Allah a dukkan al’amuran su dan samun da cewa a duniya da kuma lahira

 

Continue Reading

Labarai

Gwamnati ta rinka sayawa matasa Baburan Adaidaita – Human Right

Published

on

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Community Service Iniative ya shawarci gwamnatin Kano da ta rinka siyan baburan Adaidaita sahu tana bada su ga matukan su a kudi mai sauki domin samun sauki ga al’ummar jihar.

Shugaban kungiyar, Kwamared Balarabe Shehu Leko ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Jamhuriyya na nan gidan radiyon Dala dake zuwa a kullum da karfe 8 na dare.

Ya kuma ce, “Akwai bukatar gwamanatin ta yi kokari wajan samar da tsayayyen farashi ga masu sayar da baburan sahun da kuma masu siye su bayar haya a matsayin Hire Purchase”. A cewar Kwamared Leko.

Continue Reading

Labarai

‘Yan Jarida ku rinka watsi da labaran bogi – Kabiru Alhasan Rirum

Published

on

Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure Kabiru Alhasan Rirum ya shawarci ‘yan jaridu a jihar Kano da na kasa baki daya da su kara jajircewa wajen watsi da labaran bogi.

Dan majalisar ya bayyana hakan ne yayin wata ziyayar taya murna da ya kaiwa sabbin shugabanni kungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen jihar Kano a ranar Laraba.

Tsohon shugaban majalisar dokoki ta jihar Kano Kabiru Alhasan wanda ya sami wakilcin mataimakinsa na musamman a kan kafafen yada labarai Fatihu Yusuf Bichi ya jaddada muhimmancin ‘yan jaridun wajan sanar da al’umma labarai na gaskiya.

Ya ce ‘yan jaridu suna da rawar da zasu taka wajan raba al’umma da labarai na karya da suke futowa daga shafukan sada zumunta da sauran hanyoyi na bogi.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!