Connect with us

Labarai

WAEC: Sanya ta a takaitaccen lokaci bai dace ba – Dr Munir Kamba

Published

on

Alamu sun nuna sanarwar sanya ranar rubuta jarabawar WAEC ta zo wa dalibai a ba zata, duba da yadda a ka rinka sanya ranar a na dagewa, inda gwamnatin ta sanar da shirin komawa makaranta daga bisani kuma ta janye.

Wata uwa a jihar Kano a zantawar ta da gidan rediyon Dala Hajiya Mariya Inuwa Durumin Iya ta ce, “Lokacin da a ka sanya domin zana jarawabar WAEC ya yi kadan ga daliban, domin an riga an debe musu karsashin jarabawar saboda zaman gida na dole da a ka shafe tsawon lokaci a na yi”. Inji Hajiya Mariya Inuwa

Kafin dai tafiya hutun dole sanadiyyar barkewar annobar cutar Corona, dalibai sun riga sun kammala rajistar WAEC abun da ya rage kawai shi ne sanya rana domin fara rubuta jarrabawar.

A zantawar Dala FM, da wasu dalibai da ke shirin rubuta jarrabawar ta WAEC sun bayyana farin cikin su a kan yadda suka ji an sanya ranar rubuta jarrabawar.

Sai dai wani dan gwgawarmayar rajin kare hakkin al’umma kuwa, Kwamaret Bello Basi Fagge ya ce, “Abun farin ciki ne da godiya da gwamnati ta amince a rubuta jarrabawar, sai dai gwamnati ta gaza wajen inganta ilimin daliban a lokacin da a ke dokar cikin dokar kulle”. A cewar Kwamared Basi Fagge

A gefe guda kuma masana a bangaren ilimi a kasar nan, Dakta Munir Kamba malami a sashen nazarin adana bayanai na tsangayar ilimi ta jami’ar Bayero dake nan Kano ya ce, “Sanya ranar rubuta jarabawar a wannan takaitaccen lokaci abu ne da ko kadan bai dace ba”. Inji Dakta Munir Kamba

A kwanakin baya gwamnatin Jihar Kano ta bakin Kwamishinan ilimin jihar Sanusi Sa’idu Kiru ya bayyana alwashin da gwamnatin ta sha da cewa, ta shirya tsaf domin tunkarar jarabawar ta WAEC bayan da ta baiwa daliban jihar horo ta intanet, don haka duk lokacin da a ka sanya ranar fara jarrabawar ta WAEC to babu shakka daliban Kano za su kasance a mataki na gaba.

 

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending