Connect with us

Wasanni

Cassilas ya rataye safar hannun sa daga kama kwallo

Published

on

Tsohon dan mai tsaron ragar kungiyar Real Madrid kuma dan kasar Andulusiyya, Iker Casillas ya jingine safar hannun sa ta kamun kwallo daga harkokin tamaula.

Dan wasan mai shekaru 39 wanda ya buga wasanni 725 a Real Madrid tun ya na shekaru 16 wanda ya lashe kofin zakarun kungiyoyin nahiyar Turai guda 3 da kuma gasar La Liga guda 5 a lokacin sa.

Casillas ya kuma tallafawa kasar sa ta lashe gasar cin kofin duniya na shekarar 2010 tare da lashe gasar cin kofin nahiyar Turai na kasa da kasa har sau biyu na shekarar 2008 da kuma 2012.

Casillas ya koma kungiyar Porto a shekarar 2015, amma tun a shekarar 2019 bai kara yin atisaye ba da kungiyar sakamakon ciwon zuciya da yake fama. Sai dai a lokacin da ya farfado ya koma cikin jerin sawun masu horaswa a watan Yuli na shekarar 2019.

Casillas, ya kuma buga wasanni 156 a kungiyar Porto ya kuma lashe gasar Primera Liga sau 2 tare da kofin kasar Portugal guda 1.

Daga shekarar ya kuma bugawa kasar sa wasanni 167 tsakanin shekarar 2000 zuwa da 2016 wanda dan wasa Sergio Ramos ne kawai ya fi shi taka leda a kasar sa.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending