Connect with us

Labarai

‘Yan Bijilanti sun dawo daga yajin aiki  

Published

on

Shugaban kungiyar ‘yan sintiri ta jihar Kano, Muhammad Kabir Alhaji (MK Alhaji) ya bayyana cewa, kungiyar ‘yan sintiri wato Bijilanti a matakin jiha ba ta yi yajin aiki ba.

MK Alhaji ya bayyana hakan ne a zantawar sa da gidan rediyon Dala a safiyar Talatar nan.

Ya ce,”Jami’an mu na ‘yan sintiri da su ka yi yajin aiki na garin Zawaciki ne da ke karamar hukumar Kumbotso, kuma su ma yanzu haka tuni an sami sasanci a tsakanin juna”.

Ya kara da ce,”Aikin mu aiki ne na taimakon al’umma, domin haka babu maganar yajin aiki. A duk lokacin da a ka sa mu wata matsala tsakanin ‘yan kungiyar mu da jama’ar gari, kamata ya yi a rinka tuntubar mu, domin warware matsalar cikin gaggawa”.

Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito mana cewa, a lokacin baya ne dai jami’an Sintirin karamar hukumar Kumbotso na karkashin unguwar yankin zawachiki ne su ka tsunduma yajin aiki a baya a kan wasu matasan yankin kan bangaren harkokin shaye-shaye, wanda kuma a yanzu haka an samu masalaha.

Labarai

Matashin da ke Sansana bayan Akuya yana sakawa a TikTok ya shiga hannun hukumar Hisbah a Kano

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wani Matashi da aka yi zargin ya sansana bayan wata Akuya, a matsayin yana son ya yi suna a shafukan sada zumunta.

Mataimakin babban kwamandan hukumar Hisbah Dakta Mujahideen Aminudeen Abubakar, ya shaidawa Dala FM Kano cewar, sun kama matashin ne mai suna Shamsu Yakubu dan garin Dawakin kudu, mai shekaru 24, bayan da dagacin garinsu ya kawo korafi akansa.

Dagacin ya ce an kai ƙorafin matashin ne saboda yadda mutanen garin suka yi kokarin farmasa, bayan da aka gano bidiyonsa a shafin TikTok yana sansana bayan Akuya.

Yanzu haka hukumar ta ɗauki matakin kai matashin a fara yi masa gwajin Ƙwaƙwalwa, da kuma na ta’ammali da kayan maye.

Continue Reading

Labarai

Kisan gillar Edo: A gaggauta nemawa mutanen da aka kashe haƙƙin su, ko mu ɗauki Mataki bisa doka – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network, ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta Kano da kuma ta jihar Edo, da gaggauta neman haƙƙin Mafarautan nan ƴan asalin jihar Kano waɗanda aka yi wa kisan gilla a garin Uromi na jihar Edo.

Daraktan ƙungiyar na ƙasa Kwamared Gambo Madaki shi ne ya bayyana wa tashar Dala FM Kano, hakan a ranar Litinin, lokacin da yake tsokaci kan kisan sama da Mafarauta 16 a jihar Edo, waɗanda suka taho daga jihar Ribas za su dawo gida Kano.

Ya ce baya ga ɗaukar matakin lalubo waɗanda suka aikata rashin imanin, akwai buƙatar a ɗauki mummunan mataki akan su don daƙile afkuwar irin hakan a gaba.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ɓatabgari ne su ka damke wadanda abin ya shafa a Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas ta Jihar Edo, inda su ka ga bindigogin farauta, sai kawai su ka yanke cewa ai masu garkuwa da mutane ne, inda suka kona su da ransu a ranar Alhamis.

Lamarin dai ya jawo cece-ku-ce, inda ‘yan Najeriya da dama ke zargin gwamnati da gazawa wajen dakile irin wannan ɗaukar doka a hannu.

A cewar Gambo Madaki, baya ga batun kafa kwamiti da gwamnatin Kano ta yi akan wannan batun, ya kamata gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙara bibiyar lamarin da kan sa, don ganin an ɗauki matakin da ya dace akan kisan gillar ko kuma su ɗauki mataki bisa doka.

Continue Reading

Labarai

Mun baza jami’an mu lungu da saƙo don samar da tsaro yayin bikin Sallah a Kano – Anty Snaching Phone

Published

on

Rundunar tsaron nan da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Waya da kuma dakile Shaye-shayen kayan maye, ta Anty Snaching Phone, ta ce ta baza jami’an ta kusan dubu ɗaya da za su shiga lungu da saƙo na jihar nan, domin samar da tsaro a yayin bukukuwan ƙaramar Sallah.

Kwamandan rundunar a nan Kano Inuwa Salisu Sharaɗa ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Freedom Radio, ya kuma ce jami’an su za su yi duk mai yiyuwa wajen daƙile ayyukan ɓata garin da ke shirin tayar da hankalin al’umma yayin bikin sallar.

“Daga cikin jami’an mu da za su samar da tsaron akwai na cikin kayan mu da kuma na farin kaya, kuma sun fara bazama guraren da mu ka tura su tun cikin kin daren Asabar ɗin nan kuma za su yi aiki cikin ƙwarewa kamar yadda suka samu horo, “in ji Inuwa”.

Sharaɗa, ya kuma ce hakan na cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano ƙarkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa kulawar shugaban kwamitin karta-kwana da ke yaƙi da miyagun ɗabi’u da gwamnan ya kafa ƙarkashin Dakta Yusuf Ƙofar Mata.

Wannan dai na zuwa ne yayin da za’a gudanar da sallar Idi, ta ƙaramar Sallah a ranar Lahadin nan a Najeriya, da Jamhuriyyar Nijar da ƙasar Saudiyya, da ma wasu ƙasashen Duniya.

Continue Reading

Trending