Connect with us

Labarai

Kaduna: Majalisa ta dakatar da wasu ‘yan majalisa

Published

on

Nuna rashin da’ar wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Kaduna guda uku a zauren majalisa ya janyo masu hukuncin dakatarwa na tsawon watanni tara a ranar Talata.

‘Yan majalisar, sun hada da tsohon mataimakin shugaban majalisar Mukhtar Isa Hazo da kuma wasu ‘ƴan majalisa biyu har tsawon watanni tara.

Kwamitin ya zargi ɗan majalisa mai wakiltar Kagarko Nuhu Goro da Yusuf Liman dake wakiltar Maƙera da kuma Mukhtar Isa Hazo dake wakiltar Basawa da yunƙurin juyin mulki a majalisar.

haka zalika, kwamitin ya buƙaci wasu ‘ƴan majalisar biyar da a baya aka zarga da shiga cikin wannan juyin mulki da su rubuta takardar baiwa majalisar hakuri a shafukan manyan jaridun kasar nan a bisa laifin da suka aikata na kawo yamutsi a majalisar.

‘Ƴan majalisun da aka umarta da su bada hakurin, sun haɗa da tsohon shugaban majalisar Aminu Abdullahi Shagali da Salisu Isa da kuma Nasiru Usman, sai kuma Yusuf Salihu Kawo da kuma Abdulwahab Idris Ikara.

Labarai

Rahoto: Saurayi ya kai iyayen budurwar sa kotu kan zargin cinye masa kudade

Published

on

Wani matashi ya yi zargin iyayen budurwar sa sun karbi kudaden aure har da sadaki a hannun sa, bayan ya rage kwanaki uku a daura aure, iyayen budurwar su ka kawar da maganar auren kuma tsawon watanni ba zancen aure ko kuma dawo masa da kudaden da ya bayar.

Sai dai iyayen budurwar sun yi da’awar cewar, an je gwaji ne kafin aure saurayin ya gudu, inda shi kuma ya mayar da martanin cewar, a ranar da a ka je gwajin bai je da isassun kudi ba, shi yasa ya tafi, kuma washe gari ko da yaje gidan budurwar bijiro da zancen ta fasa auren, yanzu tsohon saurayin ta za ta aura, hakan ta sanya ya garzaya kotun shari’ar musulunci domin a bi masa hakkin sa.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mai sayen filaye ya kai karar abokin cinikin sa kotu bayan shekaru 3

Published

on

Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a unguwar Goran dutse, karkashin mai shari’a Isma’il Garba Kofar Na’isa, wani mutum mai suna Ibrahim Ishaq, ya yi karar wani mai suna Ibrahim Abba, kan cinikin wani filaye da su ka yi shekaru uku da su ka gabata.

Ibrahim Abba ya bai wa Ibrahim Ishaq motoci guda biyu shi kuma ya bashi filaye guda tara, daga bisani takaddama ta barke a tsakanin su, Ibrahiim Ishaq ya na zargin an cuce shi a cinikin, hakan ya sanya shi garzaya wa kotu.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: NAFDAC ta kama magungunan dabbobi na jabu a Kano

Published

on

Hukumar lura da ingancin abincin da magunguna ta kasa reshen jihar Kano NAFDAC, ta kai sumame wani gida a karamar hukumar Bichi, ta ka kama  wani mutum Muhammad Jamilu Sani, wanda aka samu yana hada magungunan dabbobi da allurai da ta ke zargin na jabu ne.

Shugaban hukumar Malam Shaba Muhammad ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!