Connect with us

Labarai

Sun kawo min gawar miji na sun ajiye babu bayani – Matar Mamaci

Published

on

Iyalan wani magidanci da ke aikin tuki a wani kamfani a jihar Kano sun yi karar kamfanin a kan zargin ya fita gida lafiya daga bisani su ka kawo masu gawar sa babu wani kwakkwaran bayani.

Matar magidancin mai suna Daharatu Abdullahi ta bayyanawa gidan rediyon Dala yadda al’amarin ya faru.

“Lafiya ya fita gida har ya tashi yara su ka yi sallah, su na yi masa a dawo lafiya, ina zaune sai ga wata mata tazo da suke aiki waje daya da mijinta ta ce min miji na sun yi hadari yana asibiti, ashe an gaya mata ya rasu bata gaya min ba, ina zuwa asibitin a ka ce min ya rasu, ina dawowa gida sai naga ma’aikatan kamfanin sun ajiye shi sun tafi, babu wadanda su ka zo su ka yi mana bayani, muna bukatar a nema mana hakkin mu… gawar tana asibiti za’a yi bincike”. Inji Daharatu Abdullahi

A nasa bangaren, manajan bangaren kasuwanci na Katifar Royal Form Ibrahim Adamu

ya ce, “Ma’aikacin mu ne, ranar Juma’a da misalin karfe sha biyu na rana, ina zaune sai manajan bangaren sauke kaya ta zo ta na kuka ga direba ya kawo kaya zai sauke a Store, ya na kokarin yin fakin ya taba wani waje ta ce ya ajiye motar ya gaji, ya ce ba komai ya je ya zauna, sai wani yaje ya gan shi ya na aman jini, ta bugo min waya ta ce a turo mota a zo a kai shi asibiti, a na kai shi asibiti likita ya ce ya rasu, da aka gaya mana ya rasu a ka aka dauko gawar aka kawo ta gidan”. Inji Ibrahim Adamu

Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewar, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Kiyawa ya ce, su na gudanar da bincike a kan al’amarin domin tabbatar abun da ya faru.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending