Labarai
Mu na son Ganduje ya ba mu filin wasa na Sabon Gari – ‘Yan kasuwar Sabon Gari

Sarkin Kasuwar Abubakar Rimi da akafi sani da kasuwar Sabon Gari a jihar Kano, Alhaji Nafi’u Indabo ya bukaci gwamnatin Jihar Kano da ta bai wa ‘yan kasuwar filin wasa na Kano Pillars da ke Unguwar Sabon-Gari domin ci gaban kasuwancinsu a wuraren.
Alhaji Nafi’u Indabo ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai wanda ya gudana a Kasuwar ta Abubakar Rimi.
Ya ce, “Sama da mutane dubu biyar ne gwamnatin ta tasa a wuraren kasuwancin su, kuma muna kira ga gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da ya samarwa ‘yan kasuwar jari kasancewar annobar Covid 19 ta karya jarin su”. Inji Alhaji Nafi’u Indabo
Wakilin mu Bilal Nasidi Mu’azu ya ruwaito cewa, Sarkin kasuwar ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwar da su bibiyi rancen kudi mara ruwa da babban bankin Kasa na CBN zai fara rabawa ga kananan da matsakaitan ‘Yan kasuwa nan bada jimawa ba.

Labarai
Zan gina makarantun Islamiyya da ta Boko don tunawa da Mafarautan da aka kashe a Uromi – Rurum

Ɗan majalisar Wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano, da Kibiya da Bunkure Kabiru Alhassan Rurum, ya yi alƙawarin gina makarantu guda biyu na Islamiyya da na Boko, a garin Torankawa da ke ƙaramar hukumar Bunkure, don tunawa da mafarautan da aka kashe a garin Uromi ta Jihar Edo a kwanakin baya.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin ma musamman ga ɗan majalisar Fatihu Yusuf Bichi ya aikewa Dala FM Kano, Sanarwar ta ce hakan na zuwa ne yayin da Rurum, yake jajantawa al’ummar garuruwan da Iyalan mamatan 16 da aka kashe, a garin Uromi da ke ƙaramar hukumar Essan ta jihar Edo.
Rurum ya kuma buƙaci Mafarauta daga yankin Arewa da su dakatar da zuwa kudancin kasar da sunan Farauta, don su mutane ne dake yawo da kayan daji kuma akwai banbancin yare tsakani da hakan ke sanyawa ana yawan cin zarafin su da sunan matsalar tsaro.
Honarable Kabiru Alhassan Rurum, bayan addu’o’i na musamman da ya yi ga mamatan, ya kuma bai wa iyalai da ƴan uwan su haƙurin jure rashin, tare da bai wa iyalan waɗanda kisan gillar ya rutsa da su gudunmawar Naira Miliyan Biyar, domin a ɗan yi cefanen kayan abinci.

Labarai
Za mu fara ɗaukar mataki akan masu zance a cikin Mota – Hukumar Hisbah

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta shirya tsaf wajen ganin ta kawo ƙarshen zancen da wasu Masoya suke yi a cikin Motoci, domin daƙile ɓarnar da ke yaɗuwa ta hakan a wasu lokutan.
Mataimakin babban kwamandan hukumar Hisbah a Kano, Dr. Mujahideen Aminudden, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da Dala FM Kano, a ranar Juma’a 18 ga watan Afrilun 2025.
“Ɗaukar wannan matakin ya zama dole kasancewar lamarin na neman ya zamar wa al’ummar jihar Kano alaƙakai, “in ji shi”.
Dakta Mujahidden ya kuma yi kira ga iyaye da su sanya idanu kan tarbiyyar ƴaƴan su, tare da rage buri wanda hakan ka iya kawo ƙarshen taɓarɓarewar tarbiyyar ƴaƴan nasu.

Hangen Dala
Kofar APC a bude take ga masu shiga – Abdullahi Abbas

Jamiyyar APC a Jihar Kano tace Kofar ta a bude take ga dukkanin masu son shigowa jamiyyar.
Shugaban jamiyyar na Kano Hon Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.
Abbas yace labarin dake yawo cewa akwai wadanda ke Shirin shigowa jamiyyar, su sani Kofar APCn a bude take tare da maraba ga dukkanin wadanda zasu shigo.
Koda dai Abdullahi Abbas yace shigowa APC ba zai hana tuhuma kan zargin cin hanci da rashawa ba, koma kaucewa hukumar EFCC da ICPC.
A baya bayan nan ne dai aka rinka yada cewa mabiya jamiyyar NNPP kwankwasiyya na Shirin shiga jamiyyar APC tare da madugun ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su