Connect with us

Labarai

Za mu inganta kadarorin gwamnati da a ka wofantar da su – Ganduje

Published

on

Gwamantin jihar Kano ta ce a shirye ta ke domin inganta kadarorin gwamnati da a ka kyalesu ba’a amfani da su domin samun kudin shiga.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin gabatar da taron majalisar zartarwa na mako-mako.

Gwamna Ganduje, ya karbi bakuncin kamfanoni guda biyu dake neman hadin gwiwa da gwamnatin domin inganta wasu kadarorin ta.

Kamfani na farko ya gabatar da kudiri a kan neman hadin gwiwa da gwamnatin Kano wajen mayar da tsohon kamfanin Triumph kasuwar ‘Yan canji, yayin da kuma kamfani na biyu ke neman hadin gwiwa da gwamnatin wajen sake zamantar da wurin Shakatawa na Tiga.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kuma godewa ma’aikatar ilimi mai zurfi, lafiya da muhalli bisa ga yadda su ka jajirce wajen ganin yara sun koma makaranta domin rubuta jarabawa bisa kaidojin cutar Corona.

Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta ruwaito cewa, gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje Kafin fara taron majalisar zartarwar sai da ya mika motar agajin gaggawa ga Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kano wadda Alhaji Aminu Dantata ya bada tallafin ta domin taimakon su yayin gudanar da ayyukan su.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending