Labarai
Kotu: Za’a jefe wani tsoho saboda laifin fyade

Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola da ke babbar kotun shari’ar musulunci a ƙofar kudu a jihar Kano ya yanke hukuncin jefewa ga wani tsoho ɗan kimanin shekaru saba’in.
Kotun ta samu tsohon mazaunin garin Falsa dake ƙaramar hukumar tsanyawa da laifin yiwa yarinya ƴar shekaru goma sha biyu fyade.
Kafin yanke hukuncin mai shari’a ya karantowa wanda a ke tuhuma zargin, sannan a ka bashi damar kare kansa, sai dai ya gaza kare kansa.
Haka ne ya sanya kotun ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar jefewa bayan an haƙa rami tare da sanya gangar jikinsa a ciki.
Kotun ta bai wa wanda a ke zargin damar ɗaukaka ƙara daga nan zuwa kwanaki talatin masu zuwa.

Hangen Dala
Kofar APC a bude take ga masu shiga – Abdullahi Abbas

Jamiyyar APC a Jihar Kano tace Kofar ta a bude take ga dukkanin masu son shigowa jamiyyar.
Shugaban jamiyyar na Kano Hon Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.
Abbas yace labarin dake yawo cewa akwai wadanda ke Shirin shigowa jamiyyar, su sani Kofar APCn a bude take tare da maraba ga dukkanin wadanda zasu shigo.
Koda dai Abdullahi Abbas yace shigowa APC ba zai hana tuhuma kan zargin cin hanci da rashawa ba, koma kaucewa hukumar EFCC da ICPC.
A baya bayan nan ne dai aka rinka yada cewa mabiya jamiyyar NNPP kwankwasiyya na Shirin shiga jamiyyar APC tare da madugun ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Hangen Dala
Gwamnoni sun bukaci a kawo karshen matasalar Filato

Ƙungiyar Gwamnonin kasar nan (NGF) ta buƙaci jagororin jihar Plateau su haɗa kan al’ummar jihar mai yawan al’adu da ƙabilu domin dakatar da kashe-kashen mutane da ake yawan samu a jihar.
Shugaban ƙungiyar, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Kwara – Abdulrahman Abdulrazaq, ne ya bayyana haka ranar Alhamis lokacin da ya kai ziyarar jaje.
“Muna kira da jagorori da masu faɗa a ji a duka garuruwan jihar da sauran fannoni da su haɗa hannu da gwamnan jihar wajen haɗa kan al’ummar jihar tare da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa”, in ji shugaban ƙungiyar ta NGF.
“Ya kamata shugabannin matasan al’umomin jihar su fito su haɗa kai wajen yin Allah wadai da tashin hankalin da ake samu a jihar, muna kira da a riƙa sasanta duka matsalolin da suka taso ta hanyar tattaunawa da lalama tare da girmama juna,” a cewar Abdulrahman Abdulrazaq.
Fiye da mutum 100 ne aka kashe cikin mako biyu da suka gabata, lokacin da wasu mahara suka kai hari a wasu garuruwan ƙananan hukumomin Bokkos da Bassa a jihar.
A ranar Talata ne babban sifeton ƴansandan ƙasar, Kayode Egbetokun ya ziyarci jihar inda ya sha alwashin kamo waɗanda suka ƙaddamar da kashe-kashen, da ya bayyana da na rashin imani, domin hukunta su.

Baba Suda
‘Yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki – Minista

Ministan Wutar Lantarki, Adedayo Adelabu ya bayyana cewa kimanin ’yan Najeriya miliyan 150 ne yanzu ke samun isasshiyar wutar lantarki, yayin da miliyan 80 ke da ƙarancin wutar lantarki.
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin taron sabunta sassan ministoci na 2025 da aka gudanar a Abuja, inda ya yi magana tare da ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris Malagi, da sauran masu ruwa da tsaki.
Adelabu ya bayyana cewa ci gaban ya samo asali ne daga shigar Najeriya cikin shirin “Mission 300” – wani gagarumin ƙoƙarin haɗin gwiwa na Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka (AfDB) da nufin samar da wutar lantarki ga ‘yan Afirka miliyan 300 nan da shekarar 2030.
Ƙa’idar ta tsara kyawawan manufofi don haɓaka hanyoyin samar da wutar lantarki, ƙara haɓaka makamashi da inganta hanyoyin magance matsalolin dafa abinci mai tsafta ga miliyoyin ‘yan Najeriya – wato Mission 300, kuma muna samun ci gaba mai kyau a kan wannan,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Ina mai farin cikin gaya muku cewa cikin ‘yan Afirka miliyan 300 da Bankin Duniya da AfDB ke son cimmawa, Najeriya na kan hanyar da za ta biya ƙasa da kashi 25 cikin 100, wanda ke nufin kusan ‘yan Najeriya miliyan 75. Da muka gabatar da yarjejeniyarmu, sun amince da mu.”

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su