Connect with us

Wasanni

Premier League: Liverpool da Leeds United za su fafata a wasan farko

Published

on

Mai rike da kambun gasar Firimiyar kasar Ingila, Liverpool za ta fara wasan ta na farko a gasar da kungiyar Leeds United a ranar 12 ga watan Satumba.

Wasan dai za a yi shi ne a filin wasa na Anfield, kuma wannan shi ne haduwar kungiyoyin biyu a karo na farko, tun bayan da Leeds United ta shafe tsawon shekaru 16 ba tare da ta halarci gasar Firimiya ba.

Liverpool da Leeds shi ne wasa na farko da za a yi a cikin gasar na kakar 2020-2021, bayan da a ka fitar da jerin jaddawalin a daren Alhamis.

Ga jerin yadda wasannin zai kasance:

12-08-2020

Burnley v Manchester United

Crystal Palace v Southampton

Fulham v Arsenal

Liverpool v Leeds United

Manchester City v Aston Villa

Tottenham Hotspur v Everton

West Brom v Leicester City

West Ham v Newcastle

14-08-2020

Brighton v Chelsea

Sheffield United v Wolves

Ga kuma jerin wasannin hamayya da za a yi a gasar.

  • 17 ga wata Oktoba – Everton v Liverpool
  • 5 Dismba – Tottenham Hotspur v Arsenal
  • 12 Disamba – Manchester United v Manchester City
  • 16 Janairu- Wolves v West Brom
  • 20 Fabrairu – Liverpool v Everton
  • 6 Maris- Manchester City v Manchester United
  • 13 Maris – Arsenal v Tottenham Hotspur
  • 1 Mayu – West Brom v Wolves

 

 

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending