Connect with us

Wasanni

Bayern Munich: Gnabry na daf da zama babban dan wasan gaba a duniya – Hansi Flick

Published

on

Mai horas da kungiyar Bayern Munich, Hansi Flick ya yarda da cewa dan wasan gaban kungiyar sa Serge Gnabry ya kusa zama dan wasan gaba mafi kyawu a fadin duniyar nan.

Gnabry tsohon dan wasan gaban kungiyar Arsenal, wanda tauraruwar sa ke haskakawa bayan da ya zura kwallaye biyu a ragar Lyon Laraba a gasar cin kofin kungiyoyin zakarun nahiyar Turai adaren Laraba.

Dan wasan dan kasar Jamus, yanzu haka ya zura kwallaye 23 a cikin wasanni 45 da ya fafata a kungiyar sa a wannan kakar.

Kocin ya ce“Kwallon farko da dan wasan ya ci, kwallo ce mai kyau mai jan hankali, domin kuwa yadda ya tsinci kansa a wajen tare da yin amfani da damar say a yi kokari sosai, idan mu ka duba ci gaban da ya samu a Bayern da kuma kasar sa ta Jamus, za mu iya danganta shi da cewa ya kusa zama babban dan wasan gaba a duniyar kwallon kafa, domin ya na da nagartar da a ke bukata a wajen dan wasan gaba”. Inji Hansi Flick.

A shekarar 2012 zuwa 2016 dan wasan Serge Gnabry ya buga wasani 10 kacal a Arsenal ya kuma zura kwallo daya daga nan kungiyar ta tura shi zuwa Westbrom a matsayin aro nan ma ya buga wasa daya kacal, a shekarar 2015 zuwa 2016 daga nan ya koma Werder Bremen a shekarar 2016-17 ya buga wasanni 27 ya ci kwallaye 11, a shekarar 2017 ya dawo Bayern Munich ya buga wasanni 61 ya ci kwallaye 22, daga nan ya tafi Hoffenheim a matsayin aro ya buga wasa 22 ya ci kwallaye 10, ya kuma dawo kungiyar sa a yanzu.

Ko a baya ma dai sai da kungiyar Real Madrid ta nemi daukan dan wasan gaban, saboda hazakar da yake da ita ta zura kwallaye a raga.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending