Connect with us

Wasanni

Laifukan da a ke zargin sa a kasar Girka: Ba zan bayar da hakuri ba – Harry Maguire

Published

on

Dan wasan bayan Manchester United, Harry Maguire, ya ce idan ya bayar da hakuri ga mahukuntan kasar Girka kamar ma ya yarda ya aikata laifi Kenan.

Maguire na wannan batun ne a lokacin da ya ke tattaunawa da BBC dangane da daukaka karar da ya yi a kan hukuncin da a ka yanke masa, sakamakon rikici da ya shiga tsakanin su da jami’an kasar Girka a yankin Myokonos.

Ya ce”Idan ma na bayar da hakuri, kamar na yarda cewa na yi laifin da a ke zargi na kenan, saboda haka ba zan bayar da hakuri ba, sai dai kawai ma da na sa ni da zan yi, saboda na saka magoya bayan kungiyar mu da ita kanta wani hali, kuma ina mai tabbatar da cewa har yanzu ni ban yi laifi ba. Na tsinci kai na a cikin wani mawuyacin halin da kowa zai iya tsintar kansa a ciki kuma kowane ne”.

Ko ya ka ji a lokacin da a ka yi ma duka?

“Sun dake ni a kafa ta sosai, saboda ina cikin wani yanayi na jin zafin dukan, sai da na ji tsoro a rayuwa ta sosai, kuma ‘yan uwana da mu ke tare da su ni sun a fi ji ma gaskiya a lokacin, saboda na san abun da ya faru a daren, kuma na san gaskiyar lamarin. Abun da ya sa ma na harzuka a lokacin na ji haushi sosai, shi ya san a mayar da martini, saboda nasan ina da karfi sosai. Kuma ina so na ci gaba da bugawa kasa ta wasa da kungiya ta, saboda ina kaunar su baki daya, kuma ni kai na ina kaunar kasar Girka, domin kuwa kasar da na ke kauna, kuma ita na zaba a wajen shakatawa ta”.

Dan wasan bayan ya je hutu ne da shi da kanwar sa da abokin sa da budurwar abokin sa da kuma budurwar dan wasan, wanda lamarin ya faru da su a can kasar ta Girka.

Kotun ta daure dan wasanni tsawannin watanni 13 a gidan Kurkuku, kuma daga baya ta umarci dan wasan da ya bayar da hakuri a kan a bun da ya faru. Sai dai tuni dan wasan ya daukaka kara ta hannun Lauyan sa.

Kan wannan batun ne mai horas da kasar Ingila, South Gate ya cire sunan dan wasan a wasan cancantar shiga gasar cin kofin kungiyoyin nahiyar Turai na kasa da kasa da za su fafata a kwanannan.

 

 

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending