Connect with us

Wasanni

PFA Award: ‘Yan wasan Liverpool sun mamaye kyautar gwarzon shekara

Published

on

Wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool su shida, sun shiga cikin jerin wadan da za a zaba a zakaran gwarzon dan wasa na kungiyar kwararrun ‘yan kwallon kafa na shekara ta kasar Ingila wato PFA.

Cikin ‘yan wasan sun hadar da Virgil van Dijk wanda ya lashe kyautar a bara da Jordan Henderson da Sadio Mane da kuma Trent Alexander-Arnold.

Manchester City wadda ta karkare a matsayi na biyu a gasar akwai ‘yan wasan ta biyu Kevin de Bruyne da kuma Raheem Sterling.

A bangaren mata kuwa akwai ‘yan wasan Chelsea hudu ciki akwai, Beth England da Sophie Ingle da Guro Reiten da kuma Ji So-yun.

Daga bangaren Arsenal akwai, Holder Vivianne Miedema da kuma Kim Little.

Jerin sunayen ‘yan wasan bangaren maza.

Trent Alexander-Arnold – Liverpool

Kevin de Bruyne – Manchester City

Jordan Henderson – Liverpool

Sadio Mane- Liverpool

Raheem Sterling – Manchester City

Virgil van Dijk – Liverpool

Bangaren mata akwai.

Beth England – Chelsea

Sophie Ingle – Chelsea

Kim Little – Arsenal

Vivianne Miedema – Arsenal

Guro Reiten – Chelsea

Ji So-yun – Chelsea

Bangaren ajin matasa akwai.

Tammy Abraham – Chelsea

Trent Alexander-Arnold – Liverpool

Marcus Rashford – Manchester United

Mason Greenwood – Manchester United

Mason Mount – Chelsea

Bukayo Saka – Arsenal

Bangaren mata matasa sun hadar da:

Erin Cuthbert – Chelsea

Lauren Hemp – Manchester City

Chloe Kelly – Manchester City

Georgia Stanway – Manchester City

Lauren James – Manchester United

Ellie Roebuck – Manchester City

A ranar Talata ne za a fadi sakamakon wanda ya cancanta a cikin su bayan an gudanar da zabe.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending