Connect with us

Addini

Kano: Mun bayar da kwana 40 a mayar da almajirai gidajen su – Dr. Zahra’u

Published

on

Gwamnatijn Jihar Kano za ta fara kwashi almajirai da ke barace-barace a kan Shatale-tale, da mahadar tituna a fadin jihar Kano tare da bai wa alaranmomin wa’adin kwanaki Arba’in, da su mayar da almajiaran su gidajen su.

Kwamishiniyar harkokin mata da kananan yara ta Jihar kano Dr. Zahra’u Muhammad Umar ce ta bayana hakan a wani taron manema labarai a ranar Laraba.

Ta ce, “Daukan wannan mataki ya zama dole sakamakon bayanan sirri da gwamnati ke samu na yin lalata da wasu yara mata da a ke zargin mabarata ne”.

Ta kuma ce, “A bangaren kananan al’amajirai kuwa gwamnati ta bai wa alaranmomin su kwanaki Arba’in domin mayar da su gidajen su”. A cewar Dr. Zahra’u Muhammad

Wakiliyarmu Yusuf Ali Abdullah ya ruwaito cewa, gwamnatin ba za ta saurarawa duk alaranmomin da suka bujirewa umarninta ba.

Addini

Iyaye ku kula da tarbiyyar ƴaƴan ku – Malama Fatima Tsakuwa

Published

on

Malamar addinin musulunci dake nan Kano Malama Fatima Ahmad Tsakuwa, ta shawarci mata da su ƙara himma wajen kula da tarbiyyar ƴaƴansu, tare da kuma zaburar da su mahimmancin yin addu’a a cikin wannan wata na Ramadana, domin rabauta da rahamar Ubangiji S.W.T.

Malama Fatima Ahmad Tsakuwa, ta bayyana hakan ne yayin taron bita ta musamman da gidauniyar Bango Charity Foundation ƙarƙashin Malama Fatima Yusif Mai tama, wanda gidauniyar ta shirya wa Mata, da bitar ta shafi watan Azumin Ramadana, akan yadda iyaye matan za su kula da ƴaƴan su, da ya gudana a ofishin ƙungiyar dake unguwar Sharaɗa a Kano.

Wakiliyar tashar Dala FM Kano, ta rawaito cewa malama Fatima Tsakuwa ta ce akwai buƙatar iyayen su ƙara lura da tarbiyyar ƴaƴansu, tare da yawaita karatun Al-kur’ani mai girma domin rabauta da falala a wajen Allah S.W.T.

Continue Reading

Addini

Ku gujewa saɓawa Ubangiji S.W.T, a cikin watan Azumin Ramadan – Mal. Abubakar na Madabo

Published

on

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan Sheikh Abubakar Kabiru Ibrahim, babban malami na Madabo, ya ja hankalin al’ummar Musulmi, da su kame daga saɓawa Ubangiji S.W.T, yayin watan Azumin Ramadan, domin gujewa fushin sa.

Sheikh Abubakar babban malami na Madabo, ya bayyana hakan ne yayin bikin saukar karatun Al-kur’ani mai girma, na makarantar Huzaifatu Yamani Littahafizul Qur’an Wattarbiyya Al-Islamiyya, ta gudanar karo na uku, na ɗalibai 103, yayin da suka kasance Maza 36, Mata 67, da ta gudanar cikin unguwar Ƙofar Ruwa dake ƙaramar hukumar Dala, a ranar Asabar.

Malamin ya kuma ce akwai buƙatar al’ummar Musulmi, su dage da yawaita karatun Al-kur’ani mai girma, tare da komawa ga Ubangiji S.W.T, tare da salatin Ma’aiki S.A.W, inda ya kuma yi kira ga ƴan kasuwa da su sauƙaƙa wa al’umma domin samun sauƙi daga cikin halin matsin rayuwar da suka samu kansu a ciki.

Da yake nasa jawabin shugaban makarantun na Huzaifatu Yamani a jihar Kano Mallam Anas Muhammad Madabo, ya ce kasancewar makarantun Islamiyya ba su da gata a wajen wasu mutane, sai dai a wajen Ubangiji S.W.T, akwai buƙatar masu hali su shigo wajen tallafawa domin samun damar shayar da ɗalibai ingantaccen Ilmi.

“Iyaye yadda ku ke nuna halin ko in kula da karatun ƴaƴan ku musamman wajen rashin turo su makaranta a kan lokaci, da ƙarancin biyan kuɗin makaranta sai kun dage domin ta haka ne zaku rinƙa ƙara mana ƙwarin gwiwa wajen koyar da ƴaƴan naku, “in ji Mal. Anas Madabo”.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, a nasa ɓangaren shugaban makarantar da ɗaliban suka yi saukar a ƙofar ruwa Mallam Abdullahi Sa’ed Umar, shawartar ɗalibai ya yi da su ƙara himma wajen neman Ilmin addinin da na zamani, domin zama ababen koyi a tsakanin al’umma.

Continue Reading

Addini

Zuwan Ramadan: Ku tallafawa mabuƙata bisa halin matsin rayuwar da ake ciki – Dr. Abdallah Gadan Ƙaya

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Usman Bin Affan dake unguwar Gadan Kaya Dakta Abdallah Usman Umar, ya shawarci al’umma da su ƙara ɗaɓɓaƙa taimakon masu ƙaramin ƙarfi a cikin watan Ramadana dake tafe, domin rabauta da lada a wajen All…S.W.T.

Dakta Abdallah Gadan Kaya, ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Rayuwa Abar Koyi da ya gudana a tashar Dala FM, a ranar Juma’a.

Ya ce kasancewar watan Ramadana wata ne mai ɗumbin falala, akwai buƙatar masu hali su tallafawa mabuƙata domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa.

“Mutane ku kasance masu yawaita karatun Al-kur’ani mai girma, da sauran litattafai, domin rabauta da rahamar Ubangiji S W.T, “in ji Dr. Abdallah”.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa Dakta Abdallah Gadan Ƙaya, ya ƙara da cewa, akwai buƙatar ƴan kasuwa su sauƙaƙawa al’umma bisa halin matsin rayuwar da aka samu kai yanzu a ciki domin samun sauƙi.

Continue Reading

Trending