Connect with us

Ilimi

SUBEB: Za mu gina sababbin ajujuwa da gyara wasu makarantun Kano

Published

on

Gwamantin jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan Uku, domin gina sabbin ajujuwa da kuma gyare-gyaren makarantu a fadin jihar Kano.

Shugaban hukumar Ilimin bai daya ta jihar Kano (SUBEB), Dr. Danlami Hayyo ne ya tabbatar da hakan yayin zantawar su da wakiliyar mu Zahrau Nasir.

Ya ce, “Ayyukan da za a yi sun hadar da haka rijiyoyin burtsatse a makarantu da sayen kujerun da yara za su rinka amfani da su a makarantu da sauran su”.

Ya kuma ce, “Tuni wadannan kudade su ka shiga asusun hukumar ta SUBEB wanda da zarar gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya dawo za a kaddamar da fara aikin”. A cewar Dr. Danlami Hayyo.

Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta rawaito cewa, Dr. Danlami Hayyo ya kuma ce, baya ga ware wadannan kudaden gyaran makarantun, akwai kuma Babura da gwamnatin ta saya, domin rabawa masu duba makarantu a kananan hukumomi wajen amfani da su a wuraren da motoci ba sa iya shiga.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Ilimi

Kano: Kwalejin kimiyya ta fito da sabon tsarin daukar dalibai – Kwamared Bello

Published

on

Hukumar gudanarwa ta kwalejin kimiyyar da fasaha ta Jihar Kano, ta ce sun fito da sabon tsarin bai wa dalibai guraben karatu da nufin kawo karshen kalubalen da su ke fuskanta na yawan dalibai.

Shugaban Kwalejin Kwamrade Bello Dalhatu ne ya bayyana hakan a ranar Talata a zantawarsa da gidan rediyon Dala.

Ya ce, “Kwalejin ta kuma bullo da sababbin manufofi domin ganin an tantance daliban da suka cancanta a basu gurbin karatu”. Inji Kwamrade Bello Dalhatu

Kwamrade Bello Dalhatu ya kuma yi kira ga daliban da su ka samu kan su a kwalejin da su mayar da hankali a kan karantun su.

Continue Reading

Ilimi

Kada gwamnoni su bude makarantu sai an ba su umarni – Boss Mustapha

Published

on

Gwamantin tarayya ta ce, lokacin buɗe makarantu bai yi ba, kuma tana gargaɗin gwamnonin jihohi da kada su karya dokar da ta bayar ta buɗe makarantu ba tare da sahalewar ta ba.

Shugaban kwamitin karta-kwana na fadar shugaban ƙasa da ke yaƙi da cutar Corona kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapaha ne ya bayyana hakan, a wani taro da ya gudana kan hanyoyin kaucewa cutar corona.

Ya ce, “Ba daidai ba ne gwamnatocin jihohi su bude makarantu ba tare sahalewar ta ba, sannan su ƙara shiri kan yadda za su kare dalibai tare da malaman su”. Inji Boss Mustapaha

 

Continue Reading

Ilimi

Idan a ka bude jami’o’i ba’a cika mana alkawaru ba za mu tafi yajin aiki – SSANU

Published

on

Kungiyar manyan ma’aikatan Jami’o’i ta kasa SSANU ta ce, idan har gwamnatin tarayya ta bude makarantun kasar nan ba tare da cika ma ta alkawuranta ba, shakka babu za ta tsunduma yajin aiki.

Mataimakin shugaban kungiyar Alfred Jimoh ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema Labarai a Jami’ar Ibadan.

Ya ce, “Idan har gwamnatin za ta duba yiwuwar bude makarantu to kamata ya yi ta kara nazartan biya mana bukatun mu, da nufin bai wa dalibai manyan makarantu komawa makaranta”.

Alfred Jimoh ya kuma ce, “Daga cikin bukatun ‘ya’yan kungiyar akwai biyan su alawus-alawus wanda gwamnatin ba ta biya mu ba tun daga shekara ta dubu biyu da tara zuwa yanzu”.  Inji Alfred Jimoh

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!