Connect with us

Labarai

Ganduje zai daga likafar asibitin Bichi zuwa babban asibitin kwararru

Published

on

Gwamnatin jihar Kano za ta daga likafar babban asibitin karamar hukumar Bichi zuwa babban asibitin kwararru wanda zai kunshi gadajen kwanciya kimanin dari hudu mai bangarori da dama.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan yayin ziyayar duba aiki da kuma duba yadda a ke duba marasa lafiya a asibiti na Bichi a ranar Laraba.

Ya ce, “Na yabawa ma’aikatan asibitin bisa yadda su ke gudanar da ayyukan su, kuma ina jan hankalin Ma’aikatan da ku kiyaye wajen yin amfani kayan kariya daga cutar Corona domin kiyaye lafiyar ku”. Inji Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa

Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya kuma bukaci ‘yan kwangilar da ke aikin gina sabon bangare a asibitin garin Bichi da su gaggauta kammalawa domin kuwa hakan wani kudiri ne na gwamnatin jihar Kano na ganin ta daga darajar asibitocin masarautun Kano guda hudu.

Wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara da ta ziyarci garin na Bichi ta rawaito cewar, Kwamishinan ya kara da cewa, gwamnatin jihar Kano ta kawo Na’urorin zamani da za a rika duba marasa lafiya a zamanance a asibitocin masarautun jihar Kano.

Labarai

Zaman lafiya: Majalisar dinkin duniya ta taka rawa – Farfesa Kamilu Fagge

Published

on

Masanin kimiyar siyasa a jami’ar Bayero da ke jihar Kano Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya ce majalisar dinkin duniya, ta taka rawa wajen samar da zaman lafiya a duniya.

Farfesa Kamilu Sani Fagge ya bayyana hakan yayin zantawa da wakiliyar mu Aisha Aminu Kundila a wani bangare na bikin ranar tunawa da majalisar dinkin duniya a wannan shekarar.

Ya ce, “Nijeriya ta zama mamba ce a majalisar ta dinkin duniya a 1960 a matsayin mamba ta 99”. Inji Farfesa Kamilu Sani Fagge.

Continue Reading

Labarai

Polio: Za mu dakile bullar cutar shan inna a Kano – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta ci gaba da sanya idanu, domin ganin ba a sake samun bullar cutar shan inna ba ta Polio a fadin jihar Kano.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan a yayin zantawar sa da manema labarai a wani bangaren na bikin ranar yaki da cutar shan inna ta duniya da ake gudanarwa a yau.

Ya ce, “Za mu ci gaba da gudanar da rigakafin cutar Polio a fadin jihar Kano, duk da cewa babu cutar a jihar wanda hakan zai bai wa yara kariya daga kamuwa da cutar a nan gaba”. A cewar Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa.

Sai dai ya bukaci iyaye da su ci gaba da kai yaran su, domin karbar rigakafin wanda hakan ne kadai zai taimaka wajen yaki da cutar ko da a nan gaba.

 

Continue Reading

Labarai

‘Yan sandan SARS 16 za su fuskanci hukunci sakamon zargin kisan kai

Published

on

Kwamitin shugaban kasa da ke bincike kan ayyukan ‘yan sanda ya ba da shawarar hukunta ‘yan sandan SARS 16 sakamakon zarginsu da kisan kai a jihohin kasar nan 12 har da birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun ce tun a watan Yunin shekarar da ta gabata ne kwamitin ya yi bincike kan mutanen, inda sai akwanan ne ya mikawa shugaban kasa rahoton.

Sauran wadanda aka mikawa rahoton sun hada da sufeto Janar na ‘yan sandan Muhammed Adamu da hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kasa da kuma attorney Janar na tarayya.

Jihohin da ‘yan sandan na SARS suka gudanar da ta’asar sun hada da: Akwa Ibom, Benue, Delta, Enugu, Lagos da Ogun, Rivers, Gombe, Kaduna da Kogi da kuma Kwara.

 

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!