Connect with us

Labarai

Kano: Za a kaddamar da dokar hukunta masu sare bishiyoyi – Dakta Getso

Published

on

Biyo bayan rahoton da hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA ta fitar a kwanakin baya da ke bayyana hasashen ta game da samun ambaliyar ruwa a wasu kananan hukumomi 20 na jihar Kano ya sanya gwamnatin jihar Kano ta fara dashen bishiya kimanin miliyan biyu a sassan jihar Kano da nufin magance kwararowar Hamada da zaizayar kasa gami da ambaliyar ruwa.

Dashen bishiyar dai an fara gudanar da shi a karshen watan Agustan da ya gabata karkashin ma’aikatar muhalli ta jihar kano

Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce, “Mun mayar da hanakali wajen dashen bishiyar da zata samar da katako wanda hakan zai kara habbaka tattalin arzikin”. A cewar Dakta Kabiru Ibrahim Getso

Wakiliyar mu Madina Shehu Hausawa ta rawaito cewar, Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya kuma ce, gwamnati na dab da kaddamar da dokar da za ta hukunta wadanda ke sare bishiyoyi barkatar domin kawo karshen matsalar

 

 

 

Labarai

Zan gina makarantun Islamiyya da ta Boko don tunawa da Mafarautan da aka kashe a Uromi – Rurum

Published

on

Ɗan majalisar Wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano, da Kibiya da Bunkure Kabiru Alhassan Rurum, ya yi alƙawarin gina makarantu guda biyu na Islamiyya da na Boko, a garin Torankawa da ke ƙaramar hukumar Bunkure, don tunawa da mafarautan da aka kashe a garin Uromi ta Jihar Edo a kwanakin baya.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin ma musamman ga ɗan majalisar Fatihu Yusuf Bichi ya aikewa Dala FM Kano, Sanarwar ta ce hakan na zuwa ne yayin da Rurum, yake jajantawa al’ummar garuruwan da Iyalan mamatan 16 da aka kashe, a garin Uromi da ke ƙaramar hukumar Essan ta jihar Edo.

 

Rurum ya kuma buƙaci Mafarauta daga yankin Arewa da su dakatar da zuwa kudancin kasar da sunan Farauta, don su mutane ne dake yawo da kayan daji kuma akwai banbancin yare tsakani da hakan ke sanyawa ana yawan cin zarafin su da sunan matsalar tsaro.

 

Honarable Kabiru Alhassan Rurum, bayan addu’o’i na musamman da ya yi ga mamatan, ya kuma bai wa iyalai da ƴan uwan su haƙurin jure rashin, tare da bai wa iyalan waɗanda kisan gillar ya rutsa da su gudunmawar Naira Miliyan Biyar, domin a ɗan yi cefanen kayan abinci.

Continue Reading

Labarai

Za mu fara ɗaukar mataki akan masu zance a cikin Mota – Hukumar Hisbah

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta shirya tsaf wajen ganin ta kawo ƙarshen zancen da wasu Masoya suke yi a cikin Motoci, domin daƙile ɓarnar da ke yaɗuwa ta hakan a wasu lokutan.

Mataimakin babban kwamandan hukumar Hisbah a Kano, Dr. Mujahideen Aminudden, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da Dala FM Kano, a ranar Juma’a 18 ga watan Afrilun 2025.

 

“Ɗaukar wannan matakin ya zama dole kasancewar lamarin na neman ya zamar wa al’ummar jihar Kano alaƙakai, “in ji shi”.

Dakta Mujahidden ya kuma yi kira ga iyaye da su sanya idanu kan tarbiyyar ƴaƴan su, tare da rage buri wanda hakan ka iya kawo ƙarshen taɓarɓarewar tarbiyyar ƴaƴan nasu.

Continue Reading

Hangen Dala

Kofar APC a bude take ga masu shiga – Abdullahi Abbas

Published

on

Jamiyyar APC a Jihar Kano tace Kofar ta a bude take ga dukkanin masu son shigowa jamiyyar.

 

Shugaban jamiyyar na Kano Hon Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.

 

Abbas yace labarin dake yawo cewa akwai wadanda ke Shirin shigowa jamiyyar, su sani Kofar APCn a bude take tare da maraba ga dukkanin wadanda zasu shigo.

 

Koda dai Abdullahi Abbas yace shigowa APC ba zai hana tuhuma kan zargin cin hanci da rashawa ba, koma kaucewa hukumar EFCC da ICPC.

 

A baya bayan nan ne dai aka rinka yada cewa mabiya jamiyyar NNPP kwankwasiyya na Shirin shiga jamiyyar APC tare da madugun ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Continue Reading

Trending