Connect with us

Labarai

WRECA: KEDCO na karya mana gwiwa – Dr Garba

Published

on

Shugaban hukumar bada ruwan sha na jihar kano, Dakta Garba Ahmad Kofar Wambai, ya ce, hukumar rarraba wutar lantarki ta KEDCO ta kashe musu wutar lantarki a cibiyoyin bada ruwan sha da ke Chalawa da kuma tashar ruwan sha ta Tiga a nan jihar Kano.

Dakta Garba Ahmad ya hakan ne yayin ganawar sa da tashar Dala a ranar Laraba.

Ya na mai cewa, “Muna a sarar miliyoyin Nairori a kan KEDCO sakamakon biyan su kudi da muke yi su na jawo mana asara a tashohin bada ruwan a Kano”.

Ya kuma ce, “KEDCO idan ba za ta iya bamu wuta ba, su fito su gaya mana domin daukar mataki”.

Ya kara da cewa, “Al’ummar jihar Kano su na kokawa akan matsalar ruwan sha baya zuwa wasu unguwanni a jihar nan”. Inji Dakta Garba Ahmad Kofar Wambai”.

Wakilin mu Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa, Shugaban hukumar ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da su yi hakuri za su shawo kan wannan matsala nan ba da dade waba.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Harin ‘yan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar mutane 20 a Zamfara

Published

on

Yan bindiga sun hallaka mutane 20 a wani har da suka kai garin Tungar Kwana da ke karamar hukumar Mafara a jihar ta Zamfara, bayan sun saci wasu dabbobin da jami’an tsaro suka kwato.

Kakakin ‘yan sandan jihar SP Shehu Muhammad ya bayyana hakan a zantawar sa da  wakilin mu Yusuf Ibrahim Jargaba.

Ya ce, “Tuni suka baza jami’an tsaro domin gano wadanda su ka yi kisan su fuskanci hukunci”. A cewar SP Shehu Muhammad

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Tarbiyya na taka muhimmiyar rawa wajen samun zaman lafiya – Liman

Published

on

Babban limamin masallacin juma’a na Umar Bin Khaddab da ke Dangi, Dr Yahaya Tanko ya ce, addinin musulunci addini ne na zaman lafiya, saboda haka al’umma su kiyayi tayar da husuma.

Dr Yahaya Tanko ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Tijjani Adamu.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashin da ake zargi da kashe matar sa ya sake gurfana a kotu

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ci gurfanar da mutumin nan da ake zargin ya kashe matar sa, a gaban babbar kotun jihar Kano mai lamba 7, karkashin mai shari’a Usman Na Abba.

Tun a ranar 2 ga watan Afirilu na shekarar da ta gaba aka yi zargin Aminu Inuwa ya yi amfani da wuka ya kashe matar sa mai suna Safara’u Muhammadu, kuma binne ta a cikin gidan sa, a unguwar Gwazaye Dorayi Karama da ke karamar hukumar Gwale.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!