Connect with us

Labarai

Rahoto: Jami’in damara ya samu gurbi a gidan gyaran hali

Published

on

Kotun majistret mai lamba 58 karkashin jagorancin mai shari’a Aminu Muhammad Gabari ta aike da wani Jami’in damara na Cooperate Security gidan gyaran hali.

Jami’in mai suna shehu Kursi mazaunin unguwar Diso Karamar hukumar Gwale ana zargin shi da lefin yunkurin kisan kai laifin da ya saba da sashi na 299 na kundin penal code.

Kunshin tuhumar ya bayyana cewar shehu kursi yayi amfani da wata katuwar kaca ya ratayawa wani makocinsu a wuya yana yunkurin rataye shi mutane suka shiga tsakani.

Yayin da aka karanta masa kunshin zargin ya bayyanawa kotun cewar yana fama da tabin hankali sai dai mai Sharia Aminu Gabari ya bayyana cewar ba shi ne zai ce ya na da lalura ba sai dai likitoci su tabbatar saboda haka kotun ta aike da shi zuwa makonni biyu sai a kara dawowa da shi kotu.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa, an kuma ayyana cewar, za a sanya likitocin kwakwalwa su duba lafiyar sa .

Domin jin cikakken rahotan saurari wannan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Harin ‘yan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar mutane 20 a Zamfara

Published

on

Yan bindiga sun hallaka mutane 20 a wani har da suka kai garin Tungar Kwana da ke karamar hukumar Mafara a jihar ta Zamfara, bayan sun saci wasu dabbobin da jami’an tsaro suka kwato.

Kakakin ‘yan sandan jihar SP Shehu Muhammad ya bayyana hakan a zantawar sa da  wakilin mu Yusuf Ibrahim Jargaba.

Ya ce, “Tuni suka baza jami’an tsaro domin gano wadanda su ka yi kisan su fuskanci hukunci”. A cewar SP Shehu Muhammad

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Tarbiyya na taka muhimmiyar rawa wajen samun zaman lafiya – Liman

Published

on

Babban limamin masallacin juma’a na Umar Bin Khaddab da ke Dangi, Dr Yahaya Tanko ya ce, addinin musulunci addini ne na zaman lafiya, saboda haka al’umma su kiyayi tayar da husuma.

Dr Yahaya Tanko ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Tijjani Adamu.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashin da ake zargi da kashe matar sa ya sake gurfana a kotu

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ci gurfanar da mutumin nan da ake zargin ya kashe matar sa, a gaban babbar kotun jihar Kano mai lamba 7, karkashin mai shari’a Usman Na Abba.

Tun a ranar 2 ga watan Afirilu na shekarar da ta gaba aka yi zargin Aminu Inuwa ya yi amfani da wuka ya kashe matar sa mai suna Safara’u Muhammadu, kuma binne ta a cikin gidan sa, a unguwar Gwazaye Dorayi Karama da ke karamar hukumar Gwale.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!