Connect with us

Labarai

Alkalan kotu a Kano sun koka kan rashin biyan su kudaden alawus

Published

on

Kungiyar alkalan majistret na jihar Kano ta kai kuka ofishin babban jojin Kano, akan rashin biyan su kudaden alawus da suke bin gwamnatin jihar Kano.

A yayin ziyarar kai koken, shugaban kungiyar mai shari’a Muntari Dandago ya bayyanawa babban jojin bukatar alawus din kayayyakin aikin su da suka hada a lakatayin da kwat da kuma basu bashin motoci domin saukakawa alkalai zuwa wajen aiki.

A nasa jawabin babban jojin Kano Justice Nura Sagir Umar ya ce, “Za a duba bukatar alkalan, kuma za a share musu hawaye”. A cewar Justice Nura Sagir Umar.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito cewar, sakataren kungiyar mai shari’a Mustapha Sa’adu Datti ya bayyana cewar idan aka samarwa da alkalai kyakkyawan yanayi adalci zai wanzu a tsakanin al umma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Kotu ta baiwa ‘yan sanda umarnin kama shugaban karamar hukuma a Kano

Published

on

Kotun Majistiri da ke zamanta a Gezawa karkashin mai Sharia’a Salisu Haruna Bala – Bala ta bai wa rundunar ‘yan sandan Kano umarnin kama shugaban karamar hukumar Gaya Ahmad Tashi Abdullahi da shugaban Kansiloli na Gaya Shuaibu Mai Gado Gamarya a duk inda suke.

Tunda farko ‘yan takarar kujerar shugabancin Gaya su bakwai ne suka shigar da kara a gaban kotun sakamakon zargin dukan kawo wuka da suke zargin shugaban karamar hukumar da shugaban kansiloli na Gaya sun yiwa ‘yan takara biyu a wajen tantancewa a ranar Laraba 11 ga watan Nuwanban da muke ciki.

A yayin zaman kotun na ranar Litinin mai shari’ah Salisu Haruna Bala – Bala ya saurari dukkannin bangarorin guda biyu, bayan kammala sauraron ne kuma nan take ya baiwa DPO na Gaya dana Gezawa umarnin kamo wadanda ake zargi da aikata laifi su biyu domin dankawa Kwamishinan ‘yan sandan Kano domin ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.

Wakilin mu na Kotu da ‘yan sanda Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya rawaito alkalin kotun mai Shari’a Salisu Haruna Bala –  Bala ya ce sai bayan ‘yan sanda sun kammala bincike kan lamarin sannan kotun zata sanya ranar da zata ci gaba da zaman sauraron Shari’ar domin daukar mataki na gaba.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Za mu hada kai da ‘yan Bijilante domin samar da zaman lafiya – Mai unguwa

Published

on

Sabon mai unguwar yankin Unguwar Jakada B, Dorayi Babba a karamar hukumar Gwale Alhaji Auwal Ahmad ya ce, za su hada kai da kungiyar ‘yan Sintiri ta Bijilante domin samar da zaman lafiya, da sasanci a kan kananan laifuka ba sai an kai ga zuwa wajen ‘yan sanda.

Alhaji Auwal ya bukaci hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Tijjani Adamu, bayan nada shi sabon mai unguwar yankin na unguwar Jakada.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Yadda kayan Gwanjo maganin sanyi ke tsada a bana

Published

on

Wani mai sayar da kaya maganin sanyi na gwanjo a kasuwar Kofar Wambai da ke jihar Kano Malam Saifullahi Muhammad Ya Musa ya ce, tsadar kayan sanyi na gwanjo a wannan lokacin ba laifin su ba ne, suma da tsadar su ke sayen kayan.

Malam Saifullahi ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!