Connect with us

Labarai

Hatsarin kwale-kwale: Mutane 18 sun rasu a Bauchi

Published

on

Hatsarin kwale-kwale ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18 a jihar Bauchi a Kogin Buji da ke karamar hukumar Itas Gadau.

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutanen, a cikin sanarwar da mai magana da yawun rundunar DSP Ahmed Muhammed Wakil ya fitar.

Ya ce, “Goma sha shida daga cikin wadanda suka rasa rayukansu kananan yara ne, sai dai masu aikin ceto sun samu nasarar ceto mutane biyar wadanda biyu daga cikin su suna cikin mawuyacin hali”.

Ya kuma ce, “Jirgin kwale-kwalen yana dauke ne da manoma ashirin da uku lokacin da ya yi hatsarin”. A cewar DSP Ahmed Muhammed Wakil.

Wadanda suka rasa rayukansu sun hada da, Abdulrahman Shehu, Suwaiba Yusuf, Saude Abdulkarim, Fatima Maigari, Zuwaira Maigari, Hari Maigari, Hussaina Maigari, Ummani Abdulkarim da kuma Halima Saminu.

Sauran su ne, Najaatu Hamza, Nura Abdullahi, Yahuza Abdullahi, Hafsa Abdullahi, Sadiya Hashimu, Khadija Alhassan, Amina Idris, Kaltime Hudu da kuma Furaira Malam Magaji.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Rahoto: Mu na bukatar gyaran titi a yankin mu – Unguwar Jakada

Published

on

Al’ummar Dorayi Babba unguwar Jakada sun yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta gyara musu Titin da ya tashi daga unguwar ta Jakada zuwa Rijiyar Zaki Tasha, domin ci gaba da jin dadin zirga-zirgar ababen hawa.

Al’ummar yankin sun yi kiran ne a yayin zantawar su da wakilin mu Tijjani Adamu a ranar Laraba.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rundunar ƴan sandan Kano ta cafke matashi da sinƙi-sinƙin tabar wiwi

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta cafke wani matashi a unguwar Ɗanbare ɗauke da sinƙi-sinƙin tabar wiwi, da aka sarrafa tamkar sinƙin Biredi.

Matashin ya ce, wiwin ta mahaifinsa ce, kuma yanzu an kama shi, hakan ya sa mahaifiyarsa ta umarce shi da ya sauya wa tabar wuri.

A cewar sa, mahaifin na sa ya shafe sama da shekara ashirin yana sana’ar safarar tabar wiwin.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, sun cafke matashin ne ta hanyar bayanan sirri da suka samu.

Kiyawa ya ce, tuni aka mayar da lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar ƴan sandan Kano.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Kano za ta sauyawa gidan Zoo matsuguni

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta sauya wa gidan adana namun daji na jihar matsuguni.

Kwamishinan raya al’adu da kayan tarihi na jihar Kano Ibrahim Ahmad ne ya shaida wa Freedom Radio hakan.

Kwamishinan ya ce, dalilin wannan sauyi shi ne, gidan adana namun dajin ya yi kusa da jama’a, kuma dabbobin ba sa son hayaniya.

A cewar sa, za a mayar da gidan adana namun dajin zuwa garin Tiga da ke ƙaramar hukumar Bebeji.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!