Connect with us

Manyan Labarai

Faransa: Majalisa a shirye take wajen yin dokar da za ta kare darajar Annabi – Gafasa

Published

on

Gamayyar malaman Addini da gamayyar kungiyoyi masu zaman kan sun nemi majalisar dokokin jihar Kano da ta yi dokar da za a hana koyar da darasin Faransanci a makaratun jihar Kano tare da kaucewa duk wani abu da ya shafi kasar Faransa.

Gamayyar kungiyoyin sun bayyana hakan ne ga shugaban majalisar dokokin jihar, Kano Abdul’aziz Garba Gafasa a harabar majalisar ranar Talata.

Da yake ganawa da mane labarai, Shekh Ibrahim Shehu Mai Hula ya ce”Mun zo majalisar ne a matsayin su na wakilan al’umma da su dau mataki a kan duk wanda ya taba Annabi (S.A.W) tare da janye duk wata hulda da kasar Faransa, sakamakon abun da shugaban kasar ya yi a kan Annabi tare da janye wani dan wasan kasar Faransa a Najeriya”. Inji Mai Hula.

A nasa jawabin shugaban majalisar, Abdul’aziz Garba Gafasa ya ce”Majalisar a shirye ta ke wajen yin duk wata doka da za ta kare darajar addini a matsayin mu na wakilan a’lumma kamar yadda hakin mu ne mu yi duk mai yiwuwa wajen nuna matsayar jihar Kano a kan duk wani wanda zai taba daraja Annabi (S.A.W)”. A cewar Gafasa.

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta kulle wata makaranta mai zaman kan ta a jihar

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wata makaranta mai suna Golden Crown International School a jihar, da ke yankin Sabon gari, bisa zargin an fake da sunan makarantar ana haɗa magani mara inganci mai-makon koyar da karatu a ciki.

Shugaban kwamitin yaki da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya na jihar Kano General Gambo Mai Aduwa Mai ritaya, ne ya bayyana hakan, a lokacin da Kwamitin ya kai wani sumame da karfe uku da rabi na daren jiya Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa makarantar tana kan titin Zungero da ke cikin ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano, wanda bayan samun bayanan sirri aka ɗauki matakin kulle ta.

Mai Aduwa, ya ƙara da cewar tsarin gurin ta waje ya nuna makaranta ce amma kuma sai ake sarrafa magani da ake zargin ingancin sa da bai kai yadda ya kamata ba, tare da ajiye Allurai da kayan haɗa magani cikin ajujuwan mai-makon ɗalibai.

“Za mu faɗaɗa bincike akan al’amarin dan sanin matakin da za mu ɗauka na gaba, “in ji shi”.

Suma masu gadin gurin da muka zanta da su sun bayana cewar, aikin gadi kawai suke yi amma basu da masaniyar abubuwan dake gudana a cikin makarantar, da ake zargin ana sarrafa magani mara ingani da ajiye shi a muhalin da ake zargin bai yi dai-dai da tsarin doka ba.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewa shugaban kwamitin ya ce, zai ci gaba da bibiyar guraren dake yin abubuwan da za su kawo koma baya ga harkokin lafiya, da ci gaban jihar Kano, musmman wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ƙaramar hukumar Tofa ta musanta zargin gididdiba burtalai a wasu garuruwan ta uku

Published

on

Ƙaramar hukumar Tofa ta musanta batun gididdiba burtalai a garuruwan Yanoko da Gajida da kuma Dindere, dukka a ƙaramar hukumar da ake zargin an siyarwa Manoma, domin suyi aikin Noma.

Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar ta Tofa Abubakar Sulaiman Mai Rogo, ne ya bayyana hakan a daren jiya Laraba, lokacin da yake tsokaci kan koken da Fulani Makiyaya mazauna garuruwan suka yi, kan yadda suka zargi an gididdiba burtalai a yankunan su, an siyarwa wasu Manoma, domin suyi aikin Noma, lamarin da suka ce hakan barazana ce a gare su.

Mai Rogo, ya kuma ce ƙaramar hukumar ba ta da hannu wajen gididdiba burtalai a garuruwan, yana mai cewa ko da kansilolinsa daga zuwan su bai taɓa sanin wanda ya siyar da koda kuwa kunya ɗaya ba a cikin shugabancin sa na ƙaramar hukumar domin ayi Noma, haka shima bai siyar ba.

“Yanzu haka ana kan ɗaukar matakin doka akan waɗanda suka fitar da al’amarin, kasancewar maganar tana wajen ƴan sanda, kuma ana faɗaɗa bincike, “in ji shi”.

A ziyarar gani da Ido, da tashar Dala FM Kano, ta kai wasu daga cikin burtalan da aka yi zargin an siyarwa Manoman, ta iske yadda wasu mutane suke share guraren, kamar yadda suka shaida cewa waɗanda aka siyarwa ne suka basu aikin share wajen.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, wannan na zuwa ne bayan da wasu Fulani Makiyaya mazauna garuruwan suka koka, bisa yadda suka ce an gididdiba burtalai a yankunan su, duk da wani manomi yace har takarda aka bashi bayan an siyar masa, lamarin da ya sa su cikin damuwa bisa yadda hakan ka iya sanyawa su rasa guraren da za su yi kiwon Shanun su.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gididdiba burtalan garuruwan mu da akayi ka iya haifar mana da barazana – Fulani mazauna ƙaramar hukumar Tofa

Published

on

Fulani Makiyaya na garuruwan Yanoko, da Gajida, da kuma garin Dindere da ke ƙaramar hukumar Tofa, sun koka tare da neman ɗaukin mahukunta, bisa yadda suka ce sun wayi gari da ganin wasu mutane tare da yanka burtalan garuruwan su,

Fulanin sun ce zargi ya nuna yadda aka godiddiba burtalan inda aka siyarwa da wasu shafaffu da mai, lamarin da suka ce hakan babbar barazana ce a gare su, kasancewar babu wajen da za suyi kiwon shanun su.

A zantawar Dala FM Kano, da shugaban ƙungiyar Fulani Makiyaya reshen ƙaramar hukumar Tofa, ta Gan Allah, Mallam Ahmad Shehu, ya ce gididdiba burtalan ka iya haifar musu da gagarumar matsala a rayuwa, a dan haka ne ma suke kira ga gwamnatin Kano da ta kawo musu ɗauki.

Alhaji Mamuda mazaunin Dawakin Tofa, na ɗaya daga cikin waɗanda aka yankarwa burtalin a yankin Dindere, aka kuma siyar masa, ya ce wasu ne suka siyar masa kuma an bashi takarda hakan ya sa har ya fara aiki a wajen

Wakilin dagacin garin Dindere Isah Sulaiman ya ce, lamarin yaje ga ofishin hakimin Tofa, a dan haka ne muka zanta da Turakin Tofa, Alhaji Sunusi Abubakar Tofa, kuma wakilin Makaman Bichi hakimin Tofa Alhaji Dakta Isyaku Umar Tofa, ya ce sun san da al’amarin ana ci gaba da ɗaukar mataki, kuma masarautar yankin bata bai wa kowa damar yankar burtalin ba, ko da kuwa mai unguwar Yalwal Rimi da ke garin Dindere da akace shima ya yanki burtalin.

Al’amarin gididdiba burtalin dai wasu sun danganta shi da shugabancin ƙaramar hukumar Tofa mai ci a yanzu, a dan haka ne muka yi duk mai yiyuwa wajen ji daga shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Abubakar Sulaiman Mai Goro, sai dai bai samu damar ɗaga wayar mu ba, kuma mun aike masa da saƙon karta kwana sai dai har wannan lokaci ba muji daga gareshi ba.

Continue Reading

Trending