Connect with us

Labarai

Asusun tallafawa lafiya: Najeriya za ta karbi tallafin dala milyan 143

Published

on

Najeriya za ta karbi jimillar kudi kimanin dala miliyan 143 daga asusun duniya na tallafawa harkokin lafiya wato ‘Global Fund’ don ci gaba da yaki da cutar tarin fuka.

A cewar asusun zai bai wa Najeriya kudaden ne cikin wa’adin shekaru uku masu zuwa.

Babban jami’in da ke kula da cututtuka a asusun Eliud Wanerdwalo ne ya bayyana hakan, yayin taron yaki da cutar tarin fuka karo na 33 da aka gudanar ta kafar internet.

Taron dai ya samu halartar ministocin lafiya da sauran masu ruwa da tsaki daga wasu kasashen afirka guda goma sha daya.

Ya ce, “Jimillar kudaden da asusun zai tallafawa kasashen baki daya cikin shekaru uku masu zuwa ya kai dala miliyan dari biyar, inda Najeriya ita kadai za ta samu dala miliyan dari da arba’in da uku”. A cewar Eliud Wanerdwalo.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Rahoto: Mu na bukatar gyaran titi a yankin mu – Unguwar Jakada

Published

on

Al’ummar Dorayi Babba unguwar Jakada sun yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta gyara musu Titin da ya tashi daga unguwar ta Jakada zuwa Rijiyar Zaki Tasha, domin ci gaba da jin dadin zirga-zirgar ababen hawa.

Al’ummar yankin sun yi kiran ne a yayin zantawar su da wakilin mu Tijjani Adamu a ranar Laraba.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rundunar ƴan sandan Kano ta cafke matashi da sinƙi-sinƙin tabar wiwi

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta cafke wani matashi a unguwar Ɗanbare ɗauke da sinƙi-sinƙin tabar wiwi, da aka sarrafa tamkar sinƙin Biredi.

Matashin ya ce, wiwin ta mahaifinsa ce, kuma yanzu an kama shi, hakan ya sa mahaifiyarsa ta umarce shi da ya sauya wa tabar wuri.

A cewar sa, mahaifin na sa ya shafe sama da shekara ashirin yana sana’ar safarar tabar wiwin.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, sun cafke matashin ne ta hanyar bayanan sirri da suka samu.

Kiyawa ya ce, tuni aka mayar da lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar ƴan sandan Kano.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Kano za ta sauyawa gidan Zoo matsuguni

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta sauya wa gidan adana namun daji na jihar matsuguni.

Kwamishinan raya al’adu da kayan tarihi na jihar Kano Ibrahim Ahmad ne ya shaida wa Freedom Radio hakan.

Kwamishinan ya ce, dalilin wannan sauyi shi ne, gidan adana namun dajin ya yi kusa da jama’a, kuma dabbobin ba sa son hayaniya.

A cewar sa, za a mayar da gidan adana namun dajin zuwa garin Tiga da ke ƙaramar hukumar Bebeji.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!