Connect with us

Labarai

Kwamishinan ‘yan sandan Kano ya tallafawa yara ‘yan gudun hijira

Published

on

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Habu Ahmad Sani, ya ziyarci Makarantar yara ‘yan gudun hijira da ke Mariri domin basu tallafin kayan abinci da kuma koya musu sana ‘oin dogaro da kai.

CP Habu Ahmad Sani ya kai ziyarar ne a Asabar, yayin da cika shekara daya a matsayin Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano.

Habu Ahmad Sani, ya kuma yi alkawarin ci gaba da bin duk wasu hanyoyin da tsarin aikin dan sanda ya tanadar domin kare rayuka da dukiyar jama’a.

Haka zalika, ya kuma godewa Allah da jama’ar Kano bisa hadin kai da suke bai wa rundunar ‘yan sanda wajen yaki da bata gari musamman ta hanyar bai wa rundunar sahihan bayanan sirri.

A nasa jawabin Babban malami a makarantar marayun ‘yan gudun hijira da ke Mariri Malam Usman Rabe, godewa Kwamishinan ‘Yan sandan Habu Ahmad Sani ya yi bisa tallafawa marayun.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, cikin kayan da Kwamishinan ya kaiwa marayun ‘yan gudun hijira sun hada da kayan masarufi da kayan sakawa fiye dari biyu da kuma kayan koyan sana’ar Dogaro da kai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Rahoto: Mu na bukatar gyaran titi a yankin mu – Unguwar Jakada

Published

on

Al’ummar Dorayi Babba unguwar Jakada sun yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta gyara musu Titin da ya tashi daga unguwar ta Jakada zuwa Rijiyar Zaki Tasha, domin ci gaba da jin dadin zirga-zirgar ababen hawa.

Al’ummar yankin sun yi kiran ne a yayin zantawar su da wakilin mu Tijjani Adamu a ranar Laraba.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rundunar ƴan sandan Kano ta cafke matashi da sinƙi-sinƙin tabar wiwi

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta cafke wani matashi a unguwar Ɗanbare ɗauke da sinƙi-sinƙin tabar wiwi, da aka sarrafa tamkar sinƙin Biredi.

Matashin ya ce, wiwin ta mahaifinsa ce, kuma yanzu an kama shi, hakan ya sa mahaifiyarsa ta umarce shi da ya sauya wa tabar wuri.

A cewar sa, mahaifin na sa ya shafe sama da shekara ashirin yana sana’ar safarar tabar wiwin.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, sun cafke matashin ne ta hanyar bayanan sirri da suka samu.

Kiyawa ya ce, tuni aka mayar da lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar ƴan sandan Kano.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Kano za ta sauyawa gidan Zoo matsuguni

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta sauya wa gidan adana namun daji na jihar matsuguni.

Kwamishinan raya al’adu da kayan tarihi na jihar Kano Ibrahim Ahmad ne ya shaida wa Freedom Radio hakan.

Kwamishinan ya ce, dalilin wannan sauyi shi ne, gidan adana namun dajin ya yi kusa da jama’a, kuma dabbobin ba sa son hayaniya.

A cewar sa, za a mayar da gidan adana namun dajin zuwa garin Tiga da ke ƙaramar hukumar Bebeji.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!