Connect with us

Labarai

WANI MASANI A FANIN FASAHA YA SHAWARCI GWAMNATIN TARAYYA TA GAGGAUTA ZUBA JARI A FANNIN FASAHA DON TA INGANTA TATTALIN ARZIKIN KASAR NAN

Published

on

Wani masani a fannin fasaha Mista Adetolani Eko, ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta gaggauta zuba jari a fannin fasaha don ta inganta tattalin arzikin kasar nan.
Mista Adetolani Eko ya ambata haka ne a yayin taron baje koli na fasaha karo na biyu na bana da ya guduna a jahar Legas.
Taken taron shine Samar da Ci Gaba Akan Fannin Fasaha, inda aka tattaro matasana ‘yan kasuwa hudu ba tare da yin la’akari da kudi da kuma hadaka ba don cimma burin su a fannin.
Mr Eko ya yi nuni da cewa, Gwamnatin tana da wadatattun kudin da zata iya ciyar da fannin gaba.
Kodayke yace, akwai tsare-tsare da gwamnatin ta samar don ciyar da fanninin gaba, amma duk da haka akwai bukatar gwamnati ta kara mayar da hankali wajen inganta fannin domin har yanzu akwai gibi a fannin da ba a cike ba.

Hangen Dala

Yau shugaban kasa zai dawo daga Faransa

Published

on

Bayan ziyarar aiki ta kusan mako biyu Zuwa kasar Faransa a yau litinin ake saka ran shugaban kasa zai dawo gida Nigeria.

Cikin sanarwar da hadimin shugaban kasar kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar ya ce kowa ne lokaci daga yanzu shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu zai sauka a Nigeria domin cigaban da harkokin mulkin kasar.

Continue Reading

Labarai

Zan gina makarantun Islamiyya da ta Boko don tunawa da Mafarautan da aka kashe a Uromi – Rurum

Published

on

Ɗan majalisar Wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano, da Kibiya da Bunkure Kabiru Alhassan Rurum, ya yi alƙawarin gina makarantu guda biyu na Islamiyya da na Boko, a garin Torankawa da ke ƙaramar hukumar Bunkure, don tunawa da mafarautan da aka kashe a garin Uromi ta Jihar Edo a kwanakin baya.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin ma musamman ga ɗan majalisar Fatihu Yusuf Bichi ya aikewa Dala FM Kano, Sanarwar ta ce hakan na zuwa ne yayin da Rurum, yake jajantawa al’ummar garuruwan da Iyalan mamatan 16 da aka kashe, a garin Uromi da ke ƙaramar hukumar Essan ta jihar Edo.

 

Rurum ya kuma buƙaci Mafarauta daga yankin Arewa da su dakatar da zuwa kudancin kasar da sunan Farauta, don su mutane ne dake yawo da kayan daji kuma akwai banbancin yare tsakani da hakan ke sanyawa ana yawan cin zarafin su da sunan matsalar tsaro.

 

Honarable Kabiru Alhassan Rurum, bayan addu’o’i na musamman da ya yi ga mamatan, ya kuma bai wa iyalai da ƴan uwan su haƙurin jure rashin, tare da bai wa iyalan waɗanda kisan gillar ya rutsa da su gudunmawar Naira Miliyan Biyar, domin a ɗan yi cefanen kayan abinci.

Continue Reading

Labarai

Za mu fara ɗaukar mataki akan masu zance a cikin Mota – Hukumar Hisbah

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta shirya tsaf wajen ganin ta kawo ƙarshen zancen da wasu Masoya suke yi a cikin Motoci, domin daƙile ɓarnar da ke yaɗuwa ta hakan a wasu lokutan.

Mataimakin babban kwamandan hukumar Hisbah a Kano, Dr. Mujahideen Aminudden, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da Dala FM Kano, a ranar Juma’a 18 ga watan Afrilun 2025.

 

“Ɗaukar wannan matakin ya zama dole kasancewar lamarin na neman ya zamar wa al’ummar jihar Kano alaƙakai, “in ji shi”.

Dakta Mujahidden ya kuma yi kira ga iyaye da su sanya idanu kan tarbiyyar ƴaƴan su, tare da rage buri wanda hakan ka iya kawo ƙarshen taɓarɓarewar tarbiyyar ƴaƴan nasu.

Continue Reading

Trending