Connect with us

Labarai

Jam’iyyar PDP ta dakatar da ‘dan takarar gwamnan Kano

Published

on

Jam’iyyar PDP ta dakatar da tsohon ɗan takarar gwamnan Kano Ibrahim Al’amin Little na tsawon wata guda.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar PDP na ƙaramar hukumar Nassarawa Sulaiman Mustapha Mainasara ne ya tabbatar da hakan a tattaunawar sa da Dala FM.

A cewar sa, shugabancin mazaɓar Tudunwada ne ya aike musu da takardar dakatarwar bisa zarginsa da aikata laifukan da suka saɓa da kundin tsarin mulkin jam’iyya.

Ana zargin Little da tsame kansa daga al’amuran jam’iyya sannan ya kai jam’iyyar ƙara kotu, ba tare da yin ƙorafi ga jam’iyya ba, sannan ana zarginsa da yiwa jam’iyyar zagon ƙasa a cewar Mainasara.

Har kawo lokacin haɗa wannan rahoto Alhaji Al’amin Little bai ce komai ba a kai.

Wannan rikici na cikin gida, abu ne da ya dabaibaye jam’iyyar PDP a Kano, ko a makon da ya gabata ma, tsagin Ambasada Aminu Wali ya sanar da korar tsohon gwamna Kwankwaso daga jam’iyyar.

Sai dai tsagin Kwankwaso ya yi watsi da korar da aka yi masa.

Yayin da ake rikicin shugabanci tsakanin ɓangarorin biyu, uwar jam’iyyar ta ƙasa ta ce tsagin Kwankwaso su ne halastattun shugabannin jam’iyyar.

Labarai

Rahoto: Ina zargin mai sayar da fili ya bani takardar Biredi – Wata Mata

Published

on

Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu, wata mata ta yi karar wani mutum da cinye mata Filaye guda takwas ta hanyar ba ta takardun bogi.

Sai dai kafin fara shar’ar ne kotun ta samu sanarwar dakatar da gudanar da shari’a saboda hutu da kotunan jihar Kano su ka tafi a ranar ta Talata.

Saurari wannan domin jin cikakken rahoton.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Kotunan jihar Kano na jiran umarnin tafiya hutu a rubuce – Baba Jibo

Published

on

Mai magana da yawun kotunan jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ya tabbatar da umarnin rufe kotunan jihar Kano a ranar Talata.

Sai dai Baba Jibo Ibrahim a yayin zantawarsa da wakilin Ibrahim Abdullah Sorondinki ya ce, suna jiran umarnin ne a rubuce domin sanar da kotuna da kuma sauran al’umma akan halin da ake ciki.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: ‘Yar kasuwa ta gurfana a kotu kan zargin cinye manyan Kudade

Published

on

Babbar kotun shari’ar musulunci da ke filin Hockey karkashin mai shari’a Abdullahi Halliru Abubakar, ta gurfanar da wata mata kan zargin karbar kudi Naira miliyan tara da dubu dari shida a hannun wani mutum da zummar za su yi harkar kasuwancin Dala.

Mutumin mai suna Musa Yusuf Abubakar yana karar matar mai suna Farida Usman Dantata, da cinye kudaden, wanda kuma kasancewar ranar Talatar hutu a ke yi mai shari’a bai zo ba, aka dage shari’ar zuwa ranar biyu ga watan uku shekarar 2021.

Domin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!