Connect with us

Ilimi

SHASA: Kungyar daliban Sharada ta zabi sabon jagora

Published

on

Kungiyar daliban Sharada ta zabi, Bukhari Isah Sa’id a matsayin sabon shugaba wanda zai ja ragamar kungiyar.

Zaben ya gudana ne a karshen mako karkashin masu ruwa da tsaki a harkokin karatun dalibai na jihar Kano.

Wakilin mu Tijjani Adamu ya hada mana rahoto a kan yadda zaben ya gudana.

Ilimi

Ba za mu janye komawa makaranta ba a Kano – Kwamishinan Ilimi

Published

on

Gwamnatin jihar Kano, ta tabbatar da gobe Litinin 18-01-2021 za a koma makarantu a fadin jihar baki daya.

Cikin wata sanarwa da Kwamishinan ilimi, Muhammad Sunusi Kiro ya fitar da sanarwar, cewa gwamnatin Kano za ta bude dukannin makarantun Firamare da kuma Sakandire a jihar Kano.

Ya kuma ce”Iyayen Yara da su mayar da ‘ya’yan su wadanda suke makarantun kwana a ranar Lahadin nan da mu ke ciki, gobe kuma daliban jeka ka dawo za su koma makaranta, sannan duk wani labarai da yake zagayawa cewa ba za a koma makaranta ba a gobe, zancan ba shi da tushe balle makama. Gwamnatin jihar Kano ba ta da niyar janyewa komawa makaranta a gobe”. A cewar Muhammad Sunusi Kiru.

Continue Reading

Ilimi

Rahoto: Zanga-zanga mu ka yi ba yajin aiki ba – BUK

Published

on

Ma’aikatan jami’ar Bayero a jihar Kano, sun kasance a cikin jerin ma’aikatan jami’o’in Nijeriya a kan wata zanga-zangar lumana da su ka gudanar a safiyar ranar Talata.

Gamayyar manyan ma’aikatan da kanana na SANU da kuma NASU ne su ka gudanar da Zanga-zangar a harabar sabuwar jami’ar Bayeron a jihar Kano.

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki ya halarci wajen zanga-zangar ya aiko mana rahoto daga jami’ar.

 

Continue Reading

Ilimi

SHASA: An gwangwaje kungiyar dalibai da kyautar Mota

Published

on

Sabon shugaban kungiyar daliban unguwar Sharada dake karamar hukumar birni a jihar Kano, Bukhari Isa Sa’id, ya ce ya shirya tsaf domin sauke nauyin da ya rataya a wuyan shi ga daliban yankin Sharada.

Jawabin shugaban kungiyar, Bukhari, na zuwa ne a lokacin da a ka rantsar da shi a jiya Lahadi, karkashin masu fada a ji dake yankin da kuma jihar Kano.

Ya kuma ce zai yi iya kokarin shi wajen ciyar da dukannin dalibai gaba, musamman ma a bangaren koyo da koyarwa a yankin Sharada.

Yayin taron dai wani attajiri yi wa kungiyar alkawarin kyautar Mota kyauta domin su tafikar da kungiyar a unguwar Sharada.

Ga abun da ya ke cewa da bakin shi.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!