Ilimi
Ko matashi ya san waye shi a cikin al’umma?

Na’ibin masallacin juma’a na Masjid Umar Sa’id Tudun Wada dake harabar gidan rediyon manoma a yankin unguwar Tukuntawa dake karamar hukumar birni a jihar Kano, Gwani Fasihu Gwani Dan Birni, ya ce cikakken matashi shi ne mutumin da a ka sanshi ya tashi cikin bautar Allah maimakon wata tabara da za a tsince shi a ciki.
Ya ce”“Matashi shi ne ginshikin kowace al’umma, idan sun gyaru to al’umma ta gyaru, kuma matashi shi ne jigon rayuwa ya na bukatar a ja shi a jiki a na yi masa nasiha a lokacin da aka tsince shi ya na wani abu da bai dace ba, sannan matashi ya tsaya ya yi karatun ta nutsu domin saita rayuwar sa a turbar mun tsira, idan mu ka kalli Sahabai duk matasa ne Annabawa matasa ne, saboda haka dole ne matashi ya tsaya ya yi aikin Allah wajen yin karatun alkur’ani da yin biyayya ga na gaba da shi tare da bayar da gudunmawa a cikin al’umma”.
Wakilin mu Tijjani Adamu wanda ya halarci sallar juma’a a masallacin ya rawaito mana cewa cikin hudubar Liman Gwani Fasihu Gwani Dan Birni ya mayar da hankali ne a kan matashi dungurugum a cikin hudubar Limamun.
Ilimi
Kunci da Tsanyawa: A gina mana Kwalejin kiwon lafiya – Dan Majalisa

Dan majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Kunci da Tsanyawa, Garba Ya’u Gwarmai, ya nemi gwamnatin jihar Kano da ta gina makarantar Kwalejin kiwon lafiya a yankunan su, domin ganin an samu ƙarin malaman kiwon lafiya a faɗin Kano baki ɗaya.
Garba Ya’u Gwarmai, ya bukaci hakan ne yayin zaman majalisar na ranar Talata.
Ya ce “Samar da makarantar Kwalejin kiwon lafiyar, zai ƙara inganta ilimi tare da samar da ingantaccen ilimin kiwon lafiya a yqnkin karamar hukumar dama yankin Kano ta Arewa“.
Ilimi
Adaidaita Sahu: An samu karancin fitowar dalibai da malamai a makarantun Kano

Makarantu a jihar kano sun fuskanci karancin dalibai da malamai, sakamakon yajin aikin direbobin Adaidaita Sahu suka shiga.
A zagayen da gidan rediyon Dala ya gudanar da safiyar yau Litinin zuwa wasu makarantu, mun tarar har zuwa karfe Goma na safe da yawa daga cikin makarantun babu dalibai da malamai sai ‘yan kalilan, harma a zantawar mu da wata shugabar makarantar firamare ta ce itama sai karfe Tara saura ta samu zuwa makarantar, sabo da rashin abun hawa na Adaidaita Sahu, domin haka yau ko asambile ma basu samu damar yi ba dukda cewar yau Litinin.
Wakilin mu, Ibarahim Abdullahi Sorondinki ya rawaito cewa tasgaron da yajin aikin na matuka baburan Adaidaita Sahu ya kawo, ya kuma shafi harkokin kasuwanci da ayyuka a hukumomi da ma’aikatun gwamnati da masu zaman kan su daban-daban, sakamakon rashin zuwan ma’aikatan a kan lokaci ko kuma rashin zuwan na su ma baki daya.
Ilimi
Adaidaita Sahu: Yajin aikin ya shafi daliban mu na jeka ka dawo – KSSSMB

Hukumar kula da makarantun sakandire ta jihar Kano ta ce yajin aikin da aka shiga ya shafi daliban ta na jeka ka dawo duk da cewa harka ta koyo da koyar w aba ta tsaya ba a fadin jihar Kano.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Ibrahim Baba Musa ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala a safiyar yau Litinin.
Ya ce,”Mu na fatan wannan abun da aka shiga za a samu daidaito, domin dalibai su koma bakin aiki yadda ya kamata. Kuma batun lalacewar wasu motocin daukar dalbai a Kano, daman dole ne a samu wasu sun lalace saboda zirga-zirgar yau da kulum, amma kuma wasu sun yi aiki a safiyar Litinin dinnan sun kwashi dalibai sosai, sauran kuma za a yi kokari wajen ganin gwamnati ta gyara motocin daukar daliban da su ka lalace”.
-
Manyan Labarai1 year ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi1 year ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai1 year ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi1 year ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai5 months ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi1 year ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai1 year ago
Ba’amurkiya da masoyin ta sun hada cinkoso a kasuwar Sabon Gari
-
Manyan Labarai1 year ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano