Labarai
Mutane 3 yan gida daya sun rasu sakamakon tashin gobara a Kano

Wasu mutane 3 yan gida daya sun rasu sakamakon tashin wata gobara a unguwar Rijiyar Zaki dake karamar hukumar Ungogo a daren jiya Lahadi.
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da rasuwar mutanen 3 cikin wata sanarwa da ta fitar, ta kakakinta Malam sa’idu Muhammad.
Ta ce, lamarin ya faru ne da misalign karfe 3 da minti 18 a Rumfar Shehu, kuma tana bincike domin gano musabbabin tashin gobara.
Labarai
Marayu da marasa galihu na bukatar taimakon al’umma – Limami

Wani malamin Addinin musulunci a jihar Kano ya bukaci al’umma da su dage wajen taimakawa marayu da marasa galihu dake cikin al’umma.
Limamin masallacin juma’a na Bilal Bn Rabah da ke garin Taura a Jihar Jigawa Dakta Isah Salisu Yaro ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala bude sabon masallacin juma’a na Shu’aibu Ali, dake Unguwar Ayagi a cikin karamar hukumar Dala a nan Kano.
Ya ce, “Taimakawa addini abu ne da al’ummar musulmi ya kamata su rinka a ko da yaushe”. Inji Dakta Isah Salihu.
A na sa jawabin limamin masallacin Ustaz Kabiru Sani Salihu, kira ya yi ga al’umma da su zama masu yawan godiya ga Allah (S.W.T) a kan ni’imar da ya yi wa bayin sa.
Labarai
Rahoto: A guji amfani da matasa domin tayar da rigima a wajen zabe – Limami

Limamin masallacin juma’a na Shelkwatar rundunar ‘yan sanda da ke Bompai SP Abdulkadir Haruna ya bukaci shugabanni da su guji amfani da matasa wajen tayar da hankalin al’umma a wajen zabe.
SP Abdulkadir Haruna ya bayyana hakan ne jim kadan bayan idar da sallar Juma’a, yayin da ya ke yiwa wakilin mu Abba Isah Muhammad Karin gaske akan abinda hudubar ta kunsa.
Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.
Labarai
Ya zama wajibi mu rinka yiwa tsofaffin sojoji addu’a – Ganduje

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya zama wajibi a rika yiwa tsoffin sojoji addu’a saboda sadaukar da rayuwar su wajen tabbatar da ci gaban kasar su.
Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin bikin tunawa da tsoffin sojojin da suka hidimtawa kasa.
Ya ce, “Da dama daga cikin tsoffin sojoji sun rasa rayuwar su ne wajen ganin kasar nan ta zauna lafiya da kwantar da tarzoma adon haka ya zama lallai a rika tunawa dasu da Yi musu addu’a”. A cewar Ganduje.
Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta rawaito cewa, an gudanar da faretin tunawa da tsoffin sojojin yayin taron.
-
Manyan Labarai11 months ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi1 year ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai11 months ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi1 year ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai12 months ago
Ba’amurkiya da masoyin ta sun hada cinkoso a kasuwar Sabon Gari
-
Nishadi1 year ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Labarai3 months ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Manyan Labarai12 months ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
You must be logged in to post a comment Login
You must log in to post a comment.